Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kada kuri’arsa mazabar Bourdillion, da ke Ikoyi a Jihar Legas.
Tinubu ya kada kuri’ar ne tare da rakiyar matarsa, Remi da wasu jiga-jigai na jam’iyyar.
- Gwamnan Bauchi Ya Kada Kuri’arsa, Ya Gamsu Da Kokarin Jami’an Zabe
- Motsa Jiki Na Hana Kamuwa Da Muggan Cututtuka -WHO
Ya ce, yana da cikakken kwarin guiwa na cewa shi ne zai lashe zaben shugaban kasa da ake gudanarwa.
Ya nuna gamsuwarsa kan yadda ake gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Kan fitowa jefa kuri’ar kuwa, “Muna fatan a samu fitowa sosai domin tabbatar da cigaban demokradiyya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp