Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, inda ya ce ya shirya yin “alwashi” akan wannan nasara.
Wike ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, yana mai ƙaryata hasashen tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya ce Tinubu ba zai yi nasara ba a zaɓen mai zuwa. Wike ya ce, “Ina da tabbacin Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2027. Na ji wani yana cewa zai zo na uku, ban san irin lissafin da ya yi ba. Idan zai zo na uku, to waye zai zama na farko da na biyu?”
- Wike Bai Isa Ya Hana Mu Babban Taron Jam’iyyarmu Ba – Gwamnonin PDP
- Rashin Amincewa Da Tsarin Ƴan Kudancin Kaduna Ya Sa Suka Yi Min Mummunar Fassara – El-Rufai
A ranar da ta gabata a wata hira da Channels Television, El-Rufai ya yi hasashen cewa Tinubu zai ƙare a mataki na uku a zaben 2027, yana mai cewa APC ba ta da wata hanyar kaiwa ga nasara. Ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya su ne ya kamata su tantance yadda gwamnati take gudanar da mulki da kuma irin tasirin da take yi a rayuwarsu.
Sai dai Wike ya ce siyasar ƙasar ta sauya daga lokacin zaben 2023, inda ya yi watsi da barazanar da Peter Obi na Labour Party zai iya kawo wa Shugaba Tinubu. Ya ce, “A zaben 2027, Peter Obi ba zai zama barazana ba. A 2023 ya samu ƙuri’u sama da miliyan shida, amma a 2027 lissafin siyasar zai bambanta kwata-kwata.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp