• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Dalilin Da Ya Sa Amurka Ta Hura Wutar Rikici Game Da “Yin Takara A Sararin Samaniya” Tare Da Kasar Sin A Argentina?

by CMG Hausa
2 years ago
Amurka

Shugaban hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Amurka Bill Nelson, ya ziyarci kasar Argentina a ranar 27 ga watan nan, inda a wajen wani taron manema labarai da aka yi a birnin Buenos Aires, Nelson ya ayyana nasarorin da kasar Sin ta samu wajen binciken duniyar wata, da duniyar Mars, tare da bayyana cewa, a halin yanzu Sin da Amurka suna yin takara kan harkokin sararin samaniya.

Wannan ba shi ne karon farko da manyan jami’an Amurka, suke hura wutar rikici kan batun sararin samaniya a kasar Argentina ba. A watan Maris din shekara ta 2022 ma, kwamandar rundunar sojojin Amurka dake kudancin kasar wato USSOUTHCOM, Laura Richardson, ta ziyarci Argentina, inda ta ce tashar binciken sararin samaniya mai nisa ta hadin-gwiwar Sin da Argentina dake jihar Neuquén, tasha ce ta aikin soja.

  • Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa: Tarihi Daga Cibiyar Yinxu Ta Anyang Dake Kara Fahimtar Da Sirrin Wayewar Kan Sinawa

To sai dai a nasa bangare, ministan kula da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Argentina Daniel Filmus, ya maida martani kan wannan furuci na Laura, inda ya ce, kasarsa na amfani da tashar dake jihar Neuquén don gudanar da hadin-gwiwa tare da kasar Sin ne a fannin binciken sararin samaniya da taurarin dan Adam, kamar yadda kasar take yi da kasashen Turai.

Hakikanin gaskiya, tun a shekara ta 2012, hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta Turai, ta kafa tashar binciken sararin samaniya mai nisa a Argentina, amma ko me ya sa Amurka ke zargin kasar Sin ita kadai?

Tun dai lokacin fara binciken harkokin sararin samaniya ya zuwa yanzu, kasar Sin na tsayawa kan fannin zaman lafiya. Kamar tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin da a yanzu haka take aiki a sararin samaniyar, wadda aka bude ga dukkan kasashe membobin Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan ya zama karon farko a tarihi na yin hakan. Wannan ya shaida niyyar kasar Sin na binciken sararin samaniya, wanda ba za’a iya shafa mata bakin fenti kan sa ba.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Sararin samaniya, gida ne ga daukacin al’ummar duniya, ba wai wuri ne da wata kasa ke iya nuna fin karfinta ba. Kaza lika bai kamata wasu Amurkawa, su rike tsoffin ra’ayoyinsu na da ba, kuma bai kamata a maimaita ayyukan lokacin yakin cacar baka ba, wannan ba zai yiwu ba. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Badakala A Kano: An Gano Biliyan 4 Da Ta Yi Batan-Dabo A KASCO

Badakala A Kano: An Gano Biliyan 4 Da Ta Yi Batan-Dabo A KASCO

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.