Gwamnatin kasar Sin ta fitar da kididdiga a jiya Litinin dake cewa, a watanni ukun farkon bana, yawan kudin dake shafar cinikin shige da fice na Sin ya kai kimanin dalar triliyan 1.5, adadin da ya karu da kashi 1.3% bisa makamancin lokacin bara, daga cikinsu karuwar cinikin fitar da kayayyaki ya kai kashi 6.9%, matakin da ya bayyana ingancin bunkasar Sin a wannan bangare.
Kafofin yada labarai na kasashen waje, ciki har da Bloomberg, sun labarta cewa, alkaluman cinikin Sin sun zarce hasashen da aka yi a baya duk da matakin kara kakabawa sassa daban daban harajin kwastan da Amurka ke dauka, wanda ya illata oda da dokar cinikayya ta duniya, wanda hakan ya bayyana ingancin bunkasar tattalin arzikin Sin, duk da cewa hakan bai samu cikin sauki ba.
- Amurka, Ki Fahimci Cewa “Girma Da Arziki Ke Sa A Ja Bajimin Sa Da Zaren Abawa”
- Kotu Ta Tsare Matasa 2 Kan Wallafa Bidiyon Batsa A TikTok A Kano
Tun farkon wannan wata da muke ciki, Amurka ta kakabawa sassa daban daban na duniya harajin kwastam na ramuwar gayya, matakin da ya yi matukar girgiza tsarin ciniki na duniya. Duk da hakan, Sin ta gaggauta ingiza dunkulewar hada-hadar shige da fice, inda a wani bangaren na daban take ta kokarin habaka bude kofarta ga sassan ketare.
A kwanakin nan da suka gabata kuma, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 5, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice wato Canton Fair karo na 137 a nan kasar Sin, inda yawan kamfanonin da suka halarce su suka kai matsayin koli a tarihi. Shugabar kwalejin nazarin tattalin arzikin Sin bisa salon kirkire-kirkire ta kasar Brazil madam Claudia Jannuzzi, ta ce Sin na matukar bude kofarta ga sauran sassa, tare da ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arzikin duniya.
Cinikin shige da ficen Sin na samun bunkasuwa mai dorewa a gabanin duk wani kalubale. Ba shakka duniya za ta ga hakikanin halin da ake ciki, wato babu mafita a aiwatar da manufar kariyar ciniki, illa dai a bude kofa, da hadin gwiwa ta yadda za a samu ci gaba tare. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp