Wata kotun Majistire mai lamba 7 da ke Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu matasa biyu, Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna saboda wallafa bidiyon batsa a TikTok, wanda hakan ya ci karo da addini.
Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta kai su gaban kotu, tana zargin bidiyon nasu ya saɓa da kyawawan ɗabi’u da koyarwar addini.
- Gwamnatin Kano Za Ta Sake Buɗe Makarantun Kwana 10 Don Inganta Ilimin Yara Mata
- EFCC Ta Gurfanar Da Ɗan China A Kotu Kan Bayar Da Bayanan Ƙarya
Lauyan gwamnati, Garzali Maigari Bichi, ya karanta musu zarge-zargen, amma matasan sun musanta wasu daga ciki.
Alƙalin kotun, Halima Wali, ta umarci a ci gaba da tsare su, sannan ta ɗage zaman shari’ar zuwa 24 ga watan Afrilu.
A baya, hukumar ta kama wasu da suka aikata makamancin haka a TikTok, inda aka yanke musu hukuncin shekara ɗaya a gidan gyaran hali ko biyan tara ta Naira dubu 100.
Hukumar tace fina-finai na ci gaba da yaƙi da duk wani abu da ya saɓa da tarbiyya da addini a kafafen sada zumunta a Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp