Dan wasan kwallon kafa na Liverpool Mohamed Salah ya ce, yana fatan cigaba da taka leda har lokacin da zai cika shekaru 40. A yanzu haka, yana kan tattaunawa kan yiwuwar komawarsa Saudi Pro League a nan gaba.
Dan wasan gaban Liverpool, mai shekara 32, ya yi matukar taka rawar gani a kakar wasa ta bana, inda ya zura kwallaye 29 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 18 yayin da Liverpool din ta lashe kofin Firimiya.
- CMG Ta Cimma Nasarar Gudanar Da Gasar Mutum-Mutumin Inji Ta Kasa Da Kasa
- Raya Al’adu Wani Sirri Ne Na Ci Gaban Kasar Sin
Salah ya tattaunawa da wakilansa akan yiwuwar komawa kasar Saudiya da taka leda inda ake hasashen zai samu albashin zunzurutun kudi akalla fam miliyan 500, kafin ya yanke shawarar sanya hannu kan sabon kwantiragi a Anfield a watan da ya gabata bayan cece-kucen da akai ta yi.
Da yake magana da tashar talabijin ta ON Sports, Salah ya ce “Zan daina wasa ne kawai idan na fara jin gajiya a jikina”, “Idan ka tambaye ni ra’ayi na, ina tsammanin zan iya taka leda har zuwa shekaru 39 zuwa 40 amma idan na ji ina so in daina, zan daina, na samu abubuwa da yawa a harkar kwallon kafa”, inji Salah wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Firimiya Lig ta bana.
Salah ya ci wa Liverpool da Chelsea kwallaye 186 a gasar firimiya kuma ya na matsayi na biyar a jerin wadanda suka fi kowa zura kwallo a raga inda kwallo daya kacal ta rage ya cimma tsohon dan wasan Newcastle da Manchester United Andrew Cole, dan wasan na Masar ya nuna cewa zai iya taka leda a Gabas ta Tsakiya bayan kwantiraginsa a Anfield ya kare a shekara ta 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp