Ɗan uwan shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa Jude Bellingham wanda ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Jobe Bellingham ya nuna sha’awar samun ɗaukaka kwatankwacin yadda ɗan uwan nasa ya samu a fagen ƙwallon ƙafa, wannan buri nasa ya fara cika tun ba’yan komawa Borrusia Dortmund inda Jude Bellingham ɗin ya taka leda kafin ya tafi Madrid a bazara.
Shekaru biyu ne kacal tsakanin Jude mai shekaru 21 da Jobe mai shekaru 19, Jude Bellingham ya koma Real Madrid a shekarar 2023 ba’yan shekaru uku a Dortmund, ɗan wasan tsakiyar na tawagar Ingila, Jude ya zama ɗaya daga cikin mafi kyawun ‘yan wasa a duniya a cikin ‘‘yan shekarun nan, Bellingham ƙarami ya koma Dortmund ne a watan Yuni daga Sunderland duk da cewa sun samu tikitin buga gasar Firimiya ta bana.
- Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kudiri 120 Cikin Wata Shida – Hon. Tajudeen
- Wasanmu Da Real Madrid Zai Kasance Na Musamman – Luis Enrique
“Ina da wannan burin a cikin rayuwata sannan kuma ina da dama domin har ‘yanzu ni matashi ne” Bellingham ya shaida wa manema labarai a sansanin shirye-shiryen kakar wasa na Dortmund dake Austria, ya ƙara da cewa “Wannan shawara ta zuwa Dortmund shawara ce da na ‘yanke ta ƙashin kaina wadda ba kowane zai fahimta ba”.
Bellingham ya fara buga wasansa na farko a Dortmund a gasar cin kofin duniya na ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da aka kammala a ƙasar Amurka, inda ya zura ƙwallo ɗaya kuma ya taimaka aka ci ɗaya a wasanni huɗu da ya buga, kamar yadda ya yi a Sunderland, ƙaramin Bellingham ‘yana sanya sunansa na farko Jobe a ba’yan rigarsa maimakon sunansa na ƙarshe don guje wa kamanceceniya da ɗan’uwansa.
Jobe ya ce ɗan uwansa ya ji daɗi sosai a lokacinda ya koma Dortmund inda ya kira abin a matsayin Abin Alfahari lokacin da ya gano cewa ya tafi Dortmund, ɗan wasan tsakiyar, wanda yawanci ke dannawa gaba fiye da ɗan’uwansa, ya ce ba ya son zama babban tauraro a shafukan sada zumunta “Ba na so in zama abin tattaunawa a ƙafafen sada zumunta, na fiso in zama Ɗaya daga cikin ‘‘yan wasan da suka fi hazaƙa a kowane wasa.”
Dortmund za ta buɗe kakar wasanta da Essen a zagayen farko na gasar cin kofin Jamus ranar 18 ga watan Agusta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp