Biyo bayan sanar da sakamakon zaben kujerar gwamna ba tare da kammala tattara sakamakon zaben ba da shugagaban hukumar zabe mai kanta ta kasa (INEC) ta yi a jihar Adamawa ba, gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu.
Da yake magana a wani taron manema labarai a gidan gwamnatin jihar, gwamna Fintiri yace bai yi mamakin ayyana wata ‘yar takara kafin kammala tattara sakamakon zabe da shugaban hukumar zaben Hudu Yunusa Ari yayi ba.
Ya ci gaba da “tunda muka fito zaben farko munga take-taken kwamishina Hudu Yunusa Ari, mun san zai iyayin haka, shi yasa mukayi ta kira ga INEC da ta cire shi kamar yadda ta sauke na jihar Sokoto.
“Babu sakamakon zabe a hannunsa, bai karanta komai ba, kawai yace ya baiwa wata ta zama gwamnan Adamawa, wannan shi da mahaukaci duk daya ne a wurina” inji Fintiri.
Haka kuma gwamnan ya yabawa matakin da hedikwatar hukumar zaben ta dauka kan lamarin inda yace “mu kuma a matsayinmu na shugabanni masu bin doka za mu jira mu saurari matakin da INEC za ta dauka na gaba”.
Gwamna Ahmadu Fintiri, ya kuma ki kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankulansu kuma su zauna lafiya, domin hukumar zaben za ta fidda matsayar da ya dace kan lamarin