Abokanmu, ko kun ji labarin yadda aka saci dimbin kayayyaki daga “The British Museum”, wato wurin adana kayayyakin tarihi na kasar Birtaniya? An ce wasu ma’aikatan wurin ne suka saci kayayyakin tarihi kimanin 2000, cikin tsawon shekaru 20 da suka gabata.
Sai dai a cikin kayayyakin tarihi miliyan 8 da aka adana cikin wurin, galibinsu an samo su ne daga sauran kasashe, kuma ta haramtacciyar hanya. Wato kayayyakin tarihi da suka bace dukiyoyin al’adu ne da sauran kasashe suka gada daga kaka da kakanninsu. Tabbas kasashen da aka kwacewa kayansu, da batar da su za su ji haushi sosai. Saboda haka ba mamaki ganin yadda “The British Museum” ya ji tsoro, kuma ba ya son gabatar da bayanan kayayyakin da suka bace.
Cikin kayayyakin tarihi da “The British Museum” ya mallaka, akwai kayayyakin kasar Sin da yawansu ya kai fiye da 23,000. Saboda haka, kafofin watsa labaru na kasar Sin sun mai da hankali kan labarin satar kayayyaki cikin “The British Museum”, gami da bukatar cewa a maido da dukkan kayayyakin Sin da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Najeriya ita ma ta dora muhimmanci kan lamarin, inda darektan kwamitin kula da wuraren adana kayayyakin tarihi, da tsoffin wurare masu ma’anar tarihi na kasar, Abba Tijani ya kalubalanci “The British Museum” da ya mayar da kayayyakin tagulla da aka kwashe daga daular Benin ta Najeriya.
A kan shafin yanar gizo na Internet na “The British Museum”, an rubuta cewa, akwai kayayyakin tagulla na kasar Najeriya fiye da 900 a cikin “Museum” din. Kana dukkansu an same su ne bayan da sojojin kasar Birtaniya suka kai hari kan daular Benin dake kudancin Najeriya a shekarar 1897, inda maharan suka kashe dimbin mutane, da sace dukkan kayayyaki masu daraja, gami da rushe daular ta Benin gaba daya.
A cewar “The British Museum”, bayan da bangaren Najeriya ya bukaci a mayar masa da kayayyakin da aka kwace har sau da dama, “Museum” din ya fara “musayar ra’ayi da hadin gwiwa” da Najeriya, sai dai bai ambaci yaushe zai mayar da kayayyakin ba. Ban da haka, ya ce wai wani jami’in kasar Najeriya ya ce yadda aka yi baje kolin wadannan kayayyaki a sauran kasashe, wata dabara ce ta yayata al’adun kasar Najeriya, wato “The British Museum” na neman wanke laifinsa ke nan.
Hakika, don neman kaucewa mayar da kayayyakin tarihi da ta mallaka, gwamnatin kasar Birtaniya ta dade tana amfani da dokar cikin gidanta a matsayin uzuri, kuma ta ki sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin kasa da kasa, ta yadda za ta iya magance daukar nauyin mayar da kayayyakin tarihi ga kasashen asali nasu. Kana wani tunani na tushe a bayan wadannan manufofi, a cewar kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya, shi ne: Kasashen da aka kwacewa kayayyakin daga hannunsu ba su da karfin kare kayayyakin al’adun nasu. Kana mutanen kasashen yamma suna iya kare kayayyakin, da nazari a kansu yadda ake bukata, saboda kasashen yamma cibiyar al’adu ne a wannan zamanin da muke ciki, wadanda ke ba da kariya ga al’adun dan Adam.
Ba shakka wannan tunani yana cike da girman kai. Yayin da batun gaskiya shi ne, su kasashen yamma na fuskantar raunin karfinsu a fannonin tattalin arziki da siyasa, gami da al’adu. Yanzu haka ko da kayayyakin tarihin da aka adana cikin “Museum” din ma ba za su iya kare su ba, balle ma kare al’adun dan Adam!
A sa’i daya kuma, kasashe masu tasowa sun dade suna iyakacin kokarin neman dawo da kayayyakin tarihin su, don karewa, da gadon al’adun gargajiya, tare da cimma dimbin nasarori. Misali, a bara Jamus ta mayarwa Najeriya da kayayyakin tagulla na daular Benin 20. Ko da yake kasar Jamus na ci gaba da rike kayayyakin tagullan da suka kai 1080, amma ta riga ta amince cewa, yadda ta kwaci kayayyakin daga Najeriya, da rike su a hannunta kuskure ne. Yayin da a nata bangaren, kasar Sin ta dawo da kayayyakin tarihinta fiye da 1800 gida, ta hanyar kai kara a kotu, da shawarwari, cikin shekaru 10 da suka gabata.
Dawowar kayayyakin tarihi gidajensu, na nuna karfin kasashe masu tasowa. Kana wasu al’amuran da suka auku a kwanan nan, irinsu habakar tsarin kasashen BRICS, da halartar kungiyar kasashen Afirka ta AU cikin rukunin G20 na kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya, sun nuna yadda aka tabbatar da tsarin kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya. Ta la’akari da karuwar karfin kasashe masu tasowa a kai a kai, ya kamata kasashen yamma su fara fahimtar cewa, akwai daidaito a tsakanin al’adu, da wayewar kai daban daban. Abinci nau’in “Fish & Chips” wato soyayyen kifi da dankali na kasar Birtaniya, ba zai fi tuwo da miya na Najeriya muhimmanci ba.
Hakika zamanin da muke ciki na bukatar cudanyar mabambantan al’adu maimakon rabuwar kawuna, da yadda ake koyi da juna maimakon ta da rikici, da neman kasancewa tare, maimakon baiwa wani nau’in al’adu da wayewar kai matsayi mafi muhimmanci. Wani zamani na kai hari kan sauran kasashe, da kwace kayayyakinsu, don nuna cewa wai wayewar kai ta kasashen yamma ta fi ci gaba, ya riga ya wuce tun tuni. Kana muna sa ran ganin dawowar dukkan kayayyakin tarihi da aka kwace gidajensu nan gaba ba da jimawa ba. (Bello Wang)