A yayin taron dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Larabawa da aka shirya a watan Yunin shekarar 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da wani labari kan yadda wani matashin Balarabe mai suna Mohanad Shalabi ya yi kokarin kafa da kuma bunkasa kamfaninsa a kasar Sin.
Mohanad Shalabi, wani dan kasuwa ne daga kasar Jordan, wanda ke gudanar da wani dakin cin abinci a garin Yiwu dake lardin Zhejiang.
A lokacin da isowarasa kasar Sin, Mohanad yana da mafarkin fara kasuwanci. A matsayinsa na wani Balarabe, ya yi matukar godiya ga shugaba Xi Jinping. Ya ce, kasar Sin mai bude kofofinta, na baiwa ‘yan kasashen waje damammaki da yawa, wanda hakan ya sa burinsa ya cika.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp