Shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta TikTok Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewar a kowane lokaci tana rokon Allah ya nuna mata ta shiryu daga irin ayyukan da take aikatawa kafin lokacin mutuwarta.
Murja ta bayyana haka a wani dan gajeren bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok.
- CAC Ta Bayyana Dalilan Da Ke Kawo Durkushewar Kamfanoni A Nijeriya
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas:Â Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
A kowane lokaci idan na tuna mutuwa kuma na tuna wasu daga cikin mutanen da muke tare da su amma yanzu sun mutu.
Sai inga cewar yanzu koda ace suna da wani halin banza da suke son su gyara, ba su da wannan lokacin domin sun riga sun bar Duniya.
Hakan ya sa nike rokon Sarki Allah da ya shirya ne in yi aure nima kamar sauran mutane in ganni a dakin mijina kafin lokacin mutuwata ya yi.
Ta kara da cewar daga cikin abubuwan da suke tayar mata da hankali idan ta tuna akwai kwanciyar kabari.
Idan na tuna cewar bayan na mutu dole ne za a sanya ni a cikin kabari daga ni sai aikin da na yi sai hankalina ya matukar tashi inji Murja.