YUSUF ARMAYA’U wanda aka fi sani da DR YUSUF KING mawaki ne da yake tashe, ya bayyana dalilan da suka sha bamban da na sauran kan abin da ya tsunduma shi cikin waka da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. Ga dai tattaunawarsa tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Da farko masu karatu za su so ka fara da gabatar da kanka….
Sunana Yusuf Armaya’u, wanda aka fi sani da Dr Yusuf king ko kuma Daktan waka.
Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Ni dai an haife ni a jihar Kaduna, anan nayi makaranta ta Arabi da boko, inda na karanci Rehabilitation Sciences, a yanzu ni dan kasuwa ne kuma mawaki.
Kamar wadanne irin wakoki kake yi?
Toh na kan yi wakoki irin wanda muke ce wa hikima, wato na jan hankali kenan. Sannan ina wakokin Siyasa, Biki, da Sarauta, amma na fi jin dadin yin wakar Yabo.
Wakokin fina-finai fa?
Eh! toh ban taba wakar fim ba, amma idan aka koma fannin rubutu ni marubucinta ne.
Idan na fahimce ka kana so ka ce bayan wakoki da kake yi, kana yin rubutun fim kenan, ko ya kake nufi?
Haka ne nakan yi rubutun fim ma’ana ‘Story and Screenplay’.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar waka?
Ina son idan ina magana mutane suna ba ni hankalinsu, amma a zahiri hakan bai samuwa, muddin ba ka zama wani ba. Wannan shi ya fara sani na zauna na shirya waka dan ni ma a saurari abin da zan ce game da wani abu.
Ta wacce hanya ka fara kokarin yin waka, shin ka nemi taimakon wani ko wata ko kawai da kanka ka ji ka iya ko wani ne ya koya maka?
Ita dai waka baiwa ce ba a koyanta, sai dai a nuna wa mutun ka’idojinta. Toh ni ban ma samu gatan da wani zai nuna min ka’idojinta a harkar ba, sai a hankali ta wakokin manya na fahimce su.
Ya farkon farawarka ya kasance, kamar yadda za ka ji wasu na cewa wajen dora waka ya fi basu wahala ko rubutawa, shin kai ta ya ka fara taka wakar?
An yi gwagwarmaya kafin murya ta saitu, hasali ma daga lokacin ni kadai na ke iya jin wakar tawa. Amma ni na dade ina rubuta wakoki kafin na fara rerawa, dan haka rubutun bai bani wuya ba.
Za ka yi kamar shekara nawa kana waka?
Na fara waka 2009 kin ga yanzu shekara 14 kenan.
Ko za ka iya fada wa masu karatu adadin yawan wakokin da ka yi?
Toh! ‘last 2 years’ na lissafa 80, amma ‘last year’ zuwa yanzu ban da lissafinsu sai dai na rufe dari kawai.
Ko za ka fada wa masu karatu sunayen kadan daga cikin wakokinka?
Eh! Akwai “Hikima, kar ki ji komai, Burina, A Zuciyata, Shaye-shaye, fyade, Amina, Fateema, Naseeba, Kansakali.
Da wacce waka ka fara?
Na fara da wakar Yabo wadda na yi wa Nana Fadima (A.S), inda nake cewa “Fadimatul Fauziya hanyoyin saminki da dama, jarumta har da biyayya rashinki na sa a yi kuka. Ya salamu Allah Sarki na gwani ya jalla, wanda ya kagi samai yai kassai ya ce muyi sallah, kara kara min basira in yo waka ta Battula Fadima”.
Wacce waka ce ta fi ba ka wahala cikin wakokin da kayi?
Wakar da na yi wa wani dan siyasa, wakar ta wahalar da ni sosai. Wadda nake cewa “Ga dawisu masu ado mai hali da kyan aniya, galadimar ruwan zazzau mai hali abin kwaikwaya, jagoranmu ne Dr Jafaru dan Sa’adu Ado”.
Wanne abu ne ya fi ba ka wahala cikin wakar?
Ba rubutun ba, ba kuma rerawa ba, gabatar da wakar da kuma abin da wakar ya jawo min.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da wakokinka?
Akwai su da yawa kam, Kamar; Rashin kudi a farko, domin shi kadai ne tushen daukaka, sannan rashin samun goyan bayan ‘yan uwa.
Kamar wadanne irin nasarori ka samu game da waka?
Alhamdulillah Nasarori akwai su kam, dan har duk abin da na mallaka sanadin waka ne; gida, abin hawa, shagon dana bude, da sauransu.
Wacce waka ce jama’a suka fi saninka da ita?
A fannin yabo an fi sanina da ‘we celebrating Maulidi’ a fannin hikima kuma wakata mai suna Hikima.
Wacce waka ce ta zama bakandamiyarka cikin wakokinka?
Bakandamiyata ita ce ‘Hikima’, wadda nake dewa “In ba dan hikima ba, da Dakta bai waka ba.
Ya ka dauki waka a wajenka?
Na dauke ta dabi’a, abin da turawa suke cewa Hubby, ko da kudi ko ba ta kawo min kudi zan yi, domin ina samun salama da ita.
Mu dan koma baya, ka ce kana rubutun fim, tun yaushe ka fara rubutun, kuma fim nawa ka rubuta?
Toh na fara rubutun fim shekara biyar baya, kuma na fara da fim din wani abokina ne Aminu M. Khamis, sunan fim din Ra’is.
Nawa ne adadin fina-finan da ka rubuta?
‘Home bideo’ sun kai 6 ‘season’ kuma 2.
Ko za ka fadowa masu karatu sunayensu?
Akwai; Ra’is, Fatake, Alkalami, Duhu, Matsefata, Lokaci, Sai wanda nake yi yanzu na kamfanina ‘Dare Uku’.
Me ya ja hankalinka har ka fara rubuta fim?
‘Copyright’ din mutanenmu yayi yawa, na fara rubutu ne dan kokarin karkata akalar Hausa fim industry daga satar fasahar finafinan indiya, kishin haka ya sa na shiga harkan rubutun fim.
Toh ya batun iyaye fa lokacin da ka sanar musu kana son fara yi, ko akwai wata matsala da ka fuskanta daga gare su?
A’a ban samu matsala ba sakamakon yabo na fara, daga haka kuma har nayi zurfi, sai dai saboda harkar a kasar Hausa ba a dauketa hanyar neman kudi ba, shiyasa ban sami tallafin kowa ba.
Wanne fim ka fi so cikin fina-finan da ka rubuta, kuma me ya sa?
Ra’is, Saboda irin labarin ba a taba irin sa ba a kannywood.
Me labarin ya kunsa?
Labari ne akan taimako da kyakkyawar niyya Amma daga baya abin yak oma sata kaso katsi, Soyayya ce tsakanin mutun na wani jinsin daban.
Mene ne burinka na gaba game da rubutun fim da kuma waka?
A fannin fim ina so mu kannywood mu zama ‘worldwide’ a ko’ina a ji hikima da fasahar mu, kuma idan so samu ne ta hannuna. A waka kuma ina so na kai matakin ‘international’ wato na amshi ‘Grammy award’, Ya zamana na yi ‘collaboration’ da mawakan duniya daban-daban.
Me za ka ce game da masu kuka a kan cewa shiri me dogon zango (Series film) yayi yawa a yanzu?
Zamani da kike gani kamar guguwa take, ta dauki kara da karmami, dan haka zamanin abun ne ya zo, kawai dai abin takaicin sai yanzu mutanenmu suka waye da ita, kuma suka gane tana kawo kudi shiyasa kowa ya koma kanta, amma a sannu ‘home bideo’ zai dawo.
Wanne abu ne ya fara ba ka tsoro game da waka da kuma rubutun fim?
Kabilanci, Saboda na je Legos an gaiya ce ni wakar Biki, da na je na ga manyan mawakan kudu, lokacin da aka kira ni irin kaskancin da na fuskanta sakamakon ni Bahaushe ne abin ya ba ni tsoro, hatta rawar da ake yi a kan wakata ta bambanta da tasu.
Wanne irin tunani ne ya zo maka a lokacin, wajen ganin ci gaban taka masana’antar?
Na dauki ilimi da darasi sosai, saboda su manyan mawakansu suna tallafa wa kanana, yanzu burina idan na fi haka na tallafa wa na kasana ka da su sha wuyar da na sha.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin hakan, wanda ba za ka taba iya mantawa da shi ba game da waka da kuma rubutun fim?
Na farin ciki shi ne; lokacin da ‘yan sanda suka kama wasu abokaina ni ne na je ‘bailing’ su, DPO din na ganina na sami alfarma kuma ya yi min karamci sosai, sakamakon na taba yi wa ‘yarsa wakar aure.
Ya batun aure da iyalai shin akwai ko tukunna dai?
Alhamdulillah cikin makon nan 4 ga watan march din nan aka daura min aure.
Wanne irin kalubale kuke fuskanta cikin masana’antarku musamman bangaren waka da shi kansa rubutun fim din?
Kalubale daya ne dai, tallafin da ba ma samu daga gwamnati.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga gwamnati game da ci gaban masana’antarku?
Gwamnatin nan dai tamu ce a dokar kasa ita ce uwarmu ita ce ubanmu, mafiya yawan masana’antar matasa ne, dan haka kamar nauyi ne a kanta ta tallafa mana, kullun ita ke ce mana mubar zaman banza, kuma mun daina dan haka ita ma tayi nata tallafin.
Wanne kira za ka yi game da masu kokarin fara harkar waka da kuma rubutu?
Abin da yawa amma babban abin da ya kamata su sani shi ne; harkan nan sai da kudi dan haka su nemi kudi, iya basira ba za ta kai ka ko ina ba, na biyu su jajirce kar su bari maganar kowa ya karya musu kwarin gwiwa, sannan na karshe kar su dauketa sana’a sai sun sami daukakar.
Me za ka ce da sauran ‘yan uwanka mawaka da kuma marubutan fina-fanai?
A komai mu ke yi ko za mu yi muna iya samun aljannarmu, dan haka mu kiyaye harahe ku kyautata mu’amala, kuma mu dinga tausayawa na kasanmu, mu girmana manyan mu.
Wanne sako kake da shi ga sauran al’umma baki daya?
Al’umma ina rokonku da a komai ku kyautata mana zato mu ‘ya’yanku ne, kuma danka jawo shi a jiki kake yi, muna godiya da goyan bayanmu da kuke yi.
Me za ka ce da masoyanka?
Masoyana ina godiya gare ku, idan ba ku babu ni.
Wanne irin kaya ka fi son sakawa, kuma wanne kala ka fi so?
Kaftani na fi sawa kuma fari ko sky blue.
Wanne irin abinci da abin sha ka fi so?
Duk abin da za a yi shi da doya.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Eh! akwai su, akwai shugabana madubina Sayyadi Ismail Umar Almaddah da kuma Faila United da Alhlulfaidhati Mai Diwani Group gaba daya.
Me za ka ce da wannan shafi na Rumbun Nishadi, da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Haba ai wannan shafi ya gama komai, duk wani mawaki ko dan fim karami ko babba dole ya yi alfahari da wannan shafi, babu abin da zan ce sai godiya.