FATIMA ABDULLAHI matashiyar ‘yar kasuwa mai kokarin nema na nn kanta, a cikin tattunawarsu da BILKISU TIJJANI ALKASSIM, ta bayyana irin nasarorin da ta samu a harkar kasuwancinta, gami da kira ga mata da su tashi tsaye wajen neman na kansu domin neman rufin asiri. Har ila yau, ta tabo wasu batutuwa da suka shafi rayuwa. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Fatima Abdullahi Muhammad, iyaye na haifaffun ‘yan jihar jigawa ne a cikin Karamar hukumar Hadejia. Na girma a garin Kano na yi makaranta a Kano kuma ni ce ta farko a wajen mamana da babana. Wannan ne takaitaccen tarihina.
Shin Fatima matar aure ce, ko dai ana niyya?
A’a ni bani da aure, mun dai yi niyya in sha Allah
An kusa auran kena?
Eh to kin san da ke aure mukaddari ne daga ubangiji sai ki ga wani idan ya zo babu bata lokaci an yi shi duk zaman da ka yi sai ki ga ya wuce an manta da shi. Yanzu dai gaskiya takamaimai babu maganar aure muna sa ran Allah ya kawo mana miji nagari.
‘Yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya?
Eh ni ‘yar kasuwa ce, ina saida abubuwa
Kamar wadanne irin abubuwa kie sayarwa?
Ina sai da abubuwa da dama
Shin me kasuwancin naki ya kunsa ma’ana kamar me da me kike sarrafawa?
Ina saida atamfofi, lashina, Da kuma kayan kicin, duk wani abu da kika sani na amfanin mata a kicin ina saidawa kowane iri in sha Allahu za ki samu a wajena.
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?
Eh to a gaskiya ni tun ina karama ina ganin ana kasuwanci kuma tun lokacin yake matukar burge ni har na kirma ina sha’awar kasuwanci kuma yana matukar birge ni, ni dai ina sha’awar na zama mai saye da sayarwa.
Yaya matakin karatunki?
Matakin karatuna shi ne N.C.E. daga nan na tsaya ban ci gaba ba.
Yanzu kina sha’awar ci gaba ne ko kuma kasuwancin kika sa a gaba?
Gaskiya ina da ra’ayin ci gaba da karatu kuma in sha Allahu ina sa ran hakan.
Wane irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
A gaskiya kin san ko wace sana’a ba ta rasa kalubale sai dai mu ce Alhamdu lillah. Babban kalubalena shi ne bai wuci maganar bashi ba, mutane su dauki kaya ba sa son biyan kudi, wani idan kai masa magana ya nemi ya gaya maka maganar banza kai da kayanka, wani kuma ma ba zai bayar ba sai ka zo ka yi ta rigima har ka barshi, wasu kuma ba sa san daukan kayan idan ba su da kudi wadanda ke tsoron Allah kenan, wani kuma idan ya dauka daga ya samu zai bayar. To kin gani ba za’a taba kasuwanci a ce babu bashi ba sai dai ka san wanda za ka ba wa. Allah ya bamu kasuwa mai albarka.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?
Alhamdu lillah mun samu nasarori da dama ana ta samun ci gaba, kasuwanci yana ta bunkasa sosai ma. Allah mun gode maka.
Wane abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Ina matukar jin dadi wajen biya ma kaina bukatu ba tare da na tambaya a yi min ba wannan gaskiya yana faranta min rai sosai har ma ina taimaka wa wasu Alhamdu lillah.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Kafar sada dumunta, kamar WhatsApp, Facebook, instagram, da dai sauransu.
Dame kike so mutane su rinka tunawa da ke?
Kyawawan halaye da kuma kokarin cika alkawarina, sannan idan mutum ya sayi kayana hankalina baya kwanciya har sai kayan ya shiga hannunsa ya tabbatar min da abin da ya saya ya samu.
Ga sana’a, ga kuma hidimomin yau da kullum, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
Sana’a ta na saka a gaba gaskiya, sannan kuma sana’ata ba ta hanani yin wani abu, ba ta kuma hanani hutawa.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
A ce min Allah ya jikan mahaifiyata a gaskiya duk wanda ya ce min Allah ya jikan mahaifiyata ba karamin jin dadi nake ba kuma wanda ya fada min yana shiga raina.
Wane irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Sun bani goyan baya dari bisa dari.
Kawaye fa?
Suma suna bani hadin kai sosai suna kuma taya ni tallata kayana ina gode musu.
Me kika fiso cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Cikin kayan sawa na fi son abaya ko atamfa, kayan kwalliya kuma gaskiya ni abociyar kwalliya ce ina son kowanne in dai zan yi amfani da shi ya yi min kyau to gaskiya ina son sa.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Su dage da neman na kansu, kum su rike mutuncinsu a duk inda suke. Sannan kuma su rike gaskiya da amana a kowane hali mutum ya tsinci kansa Allah zai kawo mafita.