Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce a shirye yake ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, domin amsa tuhume-tuhume 19 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ke yi masa.
Bello ya bayyana hakan ne ta bakin lauyoyinsa da suka wakilce shi a zaman kotun da aka yi a ranar Talata.
- Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Netherlands Da Saudiyya
- Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Kafa Managarcin Tsarin Kasuwar Jari
Wani daga cikin Lauyoyinsa, Mista Adeola Adedipe, SAN, ya shaida wa kotun cewa, wanda yake karewa, yana son gabatar da kansa a gaban kotu amma yana tsoron umurnin da aka bayar na cafke shi.
“Wanda ake tuhuma yana so ya zo kotu amma yana tsoron cewa akwai umarnin kama shi da ke rataye a kansa,” inji Adedipe, SAN.
Don haka, ya bukaci kotun da ta yi watsi da umarnin kama tsohon gwamnan da ta bayar a baya.