• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ina Son Kara Aure, Ko Me Yake Kawo Matsaloli Tsakanin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance?

Don Allah malam, mene ne yake kawo matsaloli tsakanin kishiyoyi, saboda ina son na kara aure?

by Dakta Jamil Zarewa
2 years ago
Aure

LABARAI MASU NASABA

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

To, malam kishi wata dabi’a ce da Allah ya halicci mata a kanta, Nana A’isha tana cewa: “Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yi wa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi (S.A.W) yana ambatonta” Bukhari 1388.

Kishi mai tsafta, shi ne: kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautata wa mijinsu, za mu iya mayar da abubuwan da suke kawo kishi mara tsafta zuwa abubuwa guda hudu, wadanda in har da za su warwaru, to da ka ji dadin zama da matanka, saboda za su zama kamar ‘yan biyu:

  1. Jahilci: Ta yadda mata da yawa suka jahilci hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar: rage yawan zawarawa da ‘yanmata, da kuma yawaita zurriyar Annabi (SAW) domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu.
  2. Mummunan zato: Yawanci uwargida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta raina ta, haka ita ma amarya takan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwargida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima. Amma idan da a ce kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba a samu matsala ba.
  3. Rashin adalci daga wajen namiji: Yawanci maza sukan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwargida za ta ce ba ta yarda ba. Sai dai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne: babu yadda za a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi (SAW) ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A’isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan kirdadi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, sai dai abin da shari’a ta hana shi ne : rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum.
  4. Munafukai masu cece-kuce: Idan da a ce kishiyoyi za su daina daukar gutsuri-tsoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli.

Idan har wadannan matsalolin za su warware, ina ganin za a samu kishi mai tsafta.

Allah ne mafi sani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Next Post
Hana Bahaya A Fili: Nijeriya Na Bukatar Ban-daki Miliyan 3.9 Duk Shekara –UNICEF

Hana Bahaya A Fili: Nijeriya Na Bukatar Ban-daki Miliyan 3.9 Duk Shekara –UNICEF

LABARAI MASU NASABA

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo

Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo

October 19, 2025
Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.