Fitacciyar Jarumar da take haskawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, da take fitowa a matsayin Uwa a cikin shirin Dadin Kowa, HAJIYA SADIYA LAWAN MUSA wadda aka fi sani da SABUWAR AYUBA, ta shafe tsawon shekaru 21 tana wasan kwaikwayo.
A wannan tattaunawar ta yi bayani dangane da yadda masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood take, ta kuma bayyana irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta wanda dalilin hakan ya sa har ta tsunduma cikin masana’antar ta Kannywood, dadin dadawa Jarumar ta yi wani karin haske dangane da masu shirya fina-finan Hausa, musamman ta yadda wasu ke yi wa masana’antar kallon Hadarin Kaji har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarta.
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Ra’ayin Yakin Cacar Baka Da Manufar Kama Karya
- Ruhin Hanyar Ruwa Ta Red Flag Zai Ci Gaba Da Kasancewa Har Abada
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi, da kuma dan takaitaccen tarihinki.
Sunana Hajiya Sadiya Lawan Musa wadda aka fi sani da Sabuwa ta Malam Ayuba a Dadin Kowa. A takaice dai ni haifaffiyar garin Kano ce, an haife ni a Gufundi, wata unguwa da ke wajejen gidan sarki, na yi firamare dina a Dala Primary School, na yi Sakandare dina a Gezawa Women’s Teachers of Gezawa, toh daga nan dai na tsaya a karatuna, sai na yi aurea takaice dai ina nan a gidan mijina kuma ina wannan harka ta fim da ‘ya’yana kuma guda bakwai.
Idan na fahimce ki kina gidanki a yanzu haka kike ci gaba da sana’arki ta fim?
Kwarai da gaske ina tare da mijina kuma ya bar ni nayi harkata ta fim duk inda zan je ya bar ni in je in yi harkokina ba shi da matsala.
Wace rawa kike takawa a cikin masana’antar Kannywood?
Ina taka rawa matsayin Uwa ta gari.
Kamar batun shirya fim ko daukar nauyi ko makamancin haka ba kya yin irinsa?
Eh! Toh gaskiya ban taba furodusin fim ba ko daraktin, amma dai ‘Ya ta ta yi Raliya wacce ta yi aure ta Dadin Kowa ita ta yi furodusin din fina-finai ma da dan dama, amma yanzu haka tayi aure tana zaune a Niger.
Raliya ‘Yar ki ce ta cikinki ko kuwa a iya shirin ne kawai?
Raliya ‘yata ce ta cikina, ita ce ta hudu cikin manyan ‘ya’yana, ni na haife ta sunanta na gaskiya Amina Lawan Musa.
Mutane za su yi mamakin ganin yadda ‘Ya da Uwa suka fito a shiri guda, me zaki ce akan hakan?
Ita rayuwar duniya duk abin da Allah ya kadarta zai faru a rayuwar mutum dole sai ya faru, toh farko dai da na fara fim a indostiri, bayan an kwana biyu sai na saka ta take yi, tana yi a Kannywood ita ma, toh ana haka ana haka kuma aka dauke ni a Dadin Kowa toh bayan an kwana biyu mun yi sabon salo toh shi ne daga baya ita ma ta nuna sha’awarta a Dadin kowan, toh shi ne aka zo akai odishen, ita ma na tura ta ta yi odishen Allah ya taimake ta kuma ta ci ita ma sai ta fara harkar ta fara shiri a Dadin kowa, ta fito a Raliya gidan Malam Barau, budurwar Razaki.
Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin harkar fim?
Abin da ya ja hankalina na tsunduma a cikin harkar nan ta fim shi ne; Matsalar rayuwace ta sa tun farko na fara shiga wannan harkar ta fim, tun da kin ga a lokacin ma da aure na, amma toh matsalar rayuwa ne, wanda wani abun sirrinka ne, toh shi ne ya sa dai a lokacin na shiga kuma Allah ya taimake ni tunda ina da ‘ya’ya a gabana ba zan iya fita na je na yi harkar banza ba na shiga harkar fim din nake dan samun abin da zan ci da ‘ya’yana, saboda lokacin mun samu matsala, mijina ya samu matsala ta rayuwa, toh shi ne abin da ya sa na shiga harkar fim din nake samun abin da nake rufawa kaina asiri da ‘ya’yana.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Toh! A kalla dai yanzu zan yi shekara 21 da shiga harkar fim.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance a wancen lokacin, kasancewar a yanzu za ki ji wasu na kuka wajen samun damar shiga masana’antar?
Toh! Gaskiya ban samu matsala ba wajen shiga masana’antar, saboda a lokacin muna tare da wadanda suke yin harkar, akwai wani yaro ma ana ce masa Baffa Sharif, darakta ne makobcina ne, a lokacin ma idan zai yi aiki ni yake kawowa aikin abincinsa da za a yi na lokeshen, kuma a lokacin ma akwai yarana kanana haka lokacin da ita Raliyar da yayanta ya ma rasu Mubarak, in za a yi fim a saka yara a ciki ya kan ce na ba shi su sai a shigar da su cikin fim din a lokacin. Toh! daga nan ne da na ga abubuwa na rayuwa suna kasancewa shi ne na yi masa magana cewar ina so na shiga harkar, sai ya ce “Toh kina ganin babu matsala, za ki iya?, sai na ce mi shi zan iya mana in Allah ya yarda toh wallahi ana fara dora min kyamera, sai suka rinka cewa “An kuwa daman baki taba yi ba?”, na ce musu ban taba yi ba, saboda komai aka saka ni zan yi shi yadda ya kamata, zan kawo abinda ake so, gaskiya ban samu matsalar shiga masana’antar ba. Sannan daga lokacin da na fara, duk wanda ya hadu da ni a wajen aikin ko darakta ko furodusa sai dai kawai na ji kira a gaba an ce mun na zo za a yi wani aikin da ni, toh a haka-a haka na bunkasa a cikin harkar nan, ba tare da an sanni a fili ba, sai dai kawai a kwalba, su kansu abokan aiki a kwalba suka fara ganina a TB, saboda ni bana zuwa ko ina, bana zuwa ofishoshin daraktoci ko furodusas ba na yawo a Zoo road din nan, ni dai kawai duk sanda za a yi aiki zan ji wani ya yi wa wani hanyata, ko a ce na ga aikin matar can ta iya da Allah ka hada ni da ita, toh ni a haka na yi ayyukana, har na zo na shiga shirin Dadin kowa.
Da yawan mutane sun fi saninki a Dadin kowa, wasu har suna ganin kamar shi ne farkon fara fim dinki, me za ki ce akan hakan?
A gaskiya dai ba Dadin Kowa na fara yi ba, na fara yin fim din Kannywood, na yi finafinai da yawa ma, na yi fina-finai sun kai kusan 50 kafin na fara yin na Dadin Kowa, na Kannywood na fara yi, kuma na yi sosai an sanni ma a fina-finan Kannywood, dan har Nijer ma da na je lokacin kafin na fara Dadin Kowa aka rinka nuna an sanni a finafinan Kannywood. Akwai wani fim nawa mana ‘Dangin Miji’, da na yi na fito a Uwar Fati Washa toh wannan shi ma fim din ya yi tashe sosai ma, saboda na fito ne a masifa a cikin fim din na yi fada sosai a fim din, toh wannan fim din ma duk inda na shiga a lokacin da shi aka sanni, a rinka cewa ga ta cikin Dangin Miji nan, amma na yi fina-finai na Kannywood sosai ma fim ma 50 kafin na fara Dadin Kowa.
Za ki iya tuna sunan fim din da kika fara yi?
Sunan fim din dana fara yi a rayuwa shi ne; Turmi Sha Daka, akwai wata kungiya ta Kano Tumbin giwa tsofaffin’yan fina-finai ne na da to da su mu kai wannan aikin, da su mu kai wannan fim din.
Ya farkon farawarki ya kasance kamar lokacin da za a fara dora miki kyamera, kasancewar shi ne farko a lokacin?
[Dariya], To farko dai da zan fara sai na rinka jin fargaba, gabana ya rinka faduwa sai da aka zo na fara sannan kuma sai na ga ashe ba wani abu bane, da ina ganin kamar ba zan iya ba a gaban mutane, kuma tun daga lokacin na samu karfin gwiwa, da zarar an dasa mun kyamera sai in ji kawai komai nawa ya zama kamar na gaske akashin dina, kamar da gaske nake yi, abin da ya sa kenan daraktoci ma suke son aktin dina kenan, sai su ce ina yin abu kamar da gaske nake yi, kuma duk sanda za a yi zan yi aktin in a gaban mutame ne na fi yin aktin sosai, sai in ji ni kamar da gaske nake kamar ba a gaban kowa nake ba. Kamar ina gaban jama’a, kamar aktin na waje ko cikin jama’a ko kofar gida ko wani abu haka dai cikin mutane toh na ma fi yin aktin din sosai.
A wanne yanayi kika fi fitowa a fim kamar matar me kudi, ko matar Talaka?
Ba wanda bana fitowa, kuma ba wanda bai dace da ni ba, idan na fito a kauye matar talaka ina dacewa saboda na iya aktin din gidan talakawa, idan kuma na fito a kushin a babban falo shi ma na iya taku saboda jikina na manyan mutane ne. Amma na fi fitowa a yanayin kauye haka ko na talakawa, na fi fitowa a talaka.
Wane ‘scene’ ne ya fi baki wuya a shirin Dadin Kowa?
[Dariya] Sin din da ya fi bani wahala shi ne; Sin din da Adama ta cije ni, shi ne abin da ya fi ba ni wuya a cikin Dadin Kowa ba na taba mantawa da wannan cizon da ta yi mun [Dariya].
Toh cizon na gaske ne kenan?
Eh! Na gaske ne. Kamar misali in aka yi wani abu na gaske, duka ko cizo ko mari ko makamancin haka, shin ana kara kudi ne fiye dana sauran da ba a yi wa ba ko kuwa duk kudi daya ne? Toh! Dai duk kudi daya ne ba a kara komai, wani zubin ma idan akai na gasken sai dai kawai a yi nishadi a yi dariya, ba a kara kudi.