Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana zaben Sanatan Zamfara ta Tsakiya da na mazabar tarayya ta Gusau/Tsafe a matsayin wanda bai kammala ba.
A nasa jawabin, jami’in zaben, Farfesa Ahmad Galadima, na Jami’ar Tarayya da ke Gusau, ya ce soke zaben ya shafi rumfuna 74 da suka fito daga kananan hukumomi 19 na Bungude, Gusau da Tsafe.
- Kwankwaso Ya Lashe Kano, Ya Bai Wa Tinubu Da Atiku Gagarumar Tazara
- Atiku Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Jihar Kebbi
Galadima ya ce jimillar katunan zaben da aka kada sun kai 43,881 wanda ya zarce adadin kuri’un da aka kada a zaben.
A cewar jami’in zaben, PDP ta samu kuri’u 93,120 sai APC, 79,444, inda aka samu tazarar kuri’u 13,676.
Shi ma a nasa jawabin, jami’in zabe na mazabar Gusau/Tsafe na tarayya, Dokta Aminu Dabai a Kaura Namoda, ya ce soke zaben ya shafi rumfunan zabe 38 daga kananan hukumomin Gusau da Tsafe.
Kuri’un da aka samu a wuraren rajista bakwai na da tazarar kuri’u a tsakanin PDP da APC wanda zarce adadin da aka tantance.
Don haka ya ce zaben mazabar tarayya na Gusau/Tsafe bai kammala ba kuma INEC za ta sake ware lokacin da za a yi sabon zabe.