Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta caccaki gwamnonin jam’iyyar PDP bisa zargin tafka magudi a zaben gwamnan Jihar Edo da aka gudanar a ranar 21 ga Satumba, 2024.
INEC ta bayyana Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 291,667, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Dakta Asue Ighodalo ya samu kuri’u 247,274. Olumide Akpata na jam’iyyar LP ya zo na uku da kuri’u 22,761.
- Me Nene Gaskiyar Tsige Sarki Sanusi Daga Kalifancin Tijjaniya A Nijeriya?
- An Samu Rarrabuwa Kan Yunƙurin Barin Damagum A Matsayin Shugaban PDP Har Zuwa 2025
Lamarin ya kunno kai ne a taron kwanaki biyu da jam’iyyar PDP ta gudanar a Jos, Jihar Filato, wanda kungiyar gwamnonin PDP ta tsaya tsayin daka, inda ta dage kan cewa magudin zabe ya hana dan takararta a Edo da kuma zargin sayen kuri’u a Ondo samun nasara.
Gwamnonin PDP sun yi zargin cewa INEC ta yi magudi wajen bai wa APC nasara a zaben gwamnan Edo.
Jam’iyyar ta yi kira ga bangaren shari’a da ‘yan majalisar dokoki da su karfafa dokokin zabe don hana abin da ta kira zagon kasa ga bukatun jama’a.
Amma da yake mayar da martani game da zargin, babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana ikirarin a matsayin abin takaici ne kuma bai dace ba.
“A matsayinmu na hukuma mai bin doka, ba za mu iya yin tsokaci kan wani lamari da ke gaban kotu ba. Lamarin yana gaban kotu, ”in ji Oyekanmi.
Ya caccaki gwamnonin PDP da bin abin da ya kira shashatan da kafafen yada labarai, inda ya bukaci jam’iyyar da ta gabatar da shaidunta a gaban kotu maimakon tayar da wasu maganganu marasa tushe a bainar jama’a.