Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gargaɗi ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa da ka da su kuskura su fara yaƙin neman zaɓen 2027.
A wata sanarwar da babban sakataren watsa labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya fitar, hukumar zaɓen ta ce ba ta fitar da jadawalin yadda zaɓen 2027 zai guda ba, don haka dukkanin wani yaƙin neman zaɓen a halin yanzu ya saɓa wa doka.
- Buƙatar Rijistar Sabbin Jam’iyyu Ta Kai 144 — INEC
- 2027: Kungiyoyi 110 Ne Ke Neman Rajistan Zama Jam’iyyun Siyasa A Yanzu Haka – INEC
“Hukumar zaɓe mai zaman kanta har yanzu ba ta fitar da jadawalin yadda babban zaɓen 2027 zai gudana ba. Don haka, ba wata jam’iyyar siyasa da za ta gudanar da zaɓen fitar da gwani ko tsayar da ɗan takara domin zaɓe,” sanarwar ta shaida.
Da take dogara da sashin dokar zaɓe ta sashi na 94(1), sanarwar ta tunatar da ‘yan siyasa cewa ba a lamunce wa kowa yin gangamin yaƙin neman zaɓen ba kafin kwanaki 150 da ranar yin zaɓe ba, kuma dole ne a kammala gangamin kafin awannin 24 da fara ka da ƙuri’ar zaɓe.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa sashi ta 95(1) na dokar zaɓe, ya ce dole dukkanin yaƙin neman zaɓe ya tafi daidai da dokokin INEC.
“Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba.
“INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin ‘yan siyasa da su bi dokoki da ƙa’idojin zaɓe,” sanarwar ta shaida.
Ya buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta matakan zaɓe tare da jiran jadawalin yadda zaɓen zai gudana a hukumance kafin su fara harkokin yaƙin neman zaɓe.
Wannan gargaɗin dai na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yadda jama’a suke ayyana goyon bayan tazarcen Shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma yadda hotunansa suke bazuwa da ake ta amincewa da tazarcensa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp