• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Gayyaci ‘Yan Takara Su Sake Rattaba Hannu Kan Zaman Lafiya Ranar Laraba

by Sulaiman
3 years ago
INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa za su bayyana a ranar Laraba, domin su sa hannu kan yarjejeniyar amincewar yarda a gudanar da zaɓe lami lafiya, ba tare da tashin hankali ba.

Yakubu ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da ‘yan jarida, bayan ya kai ziyara Makarantar Sakandire ta Garki, Abuja, inda ake bayar da horo ga Masu Sa-ido Kan Jami’an Zaɓe (SPO).

  • Karancin Kudi Ba Zai Shafi Zaben 2023 Ba —INEC 

Shugaban na INEC ya kuma kai irin wannan ziyarar a Cibiyar Taro ta Duniya (ICC), inda ya ce a can ne jihohi za su riƙa aikawa da sakamakon zaɓe ana tattarawa. Daga ƙarshe kuma a can ne shugaban na INEC zai bayyana ɗan takarar da ya yi nasara, tare da sakamakon da kowane ɗan takara ya samu.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

Yakubu ya ce haka kuma ICC zai kasance Cibiyar Yaɗa Labarai.

Haka kuma Yakubu ya ce INEC ba za ta fuskanci matsalar ƙarancin kuɗi ba, bisa dogaro da alƙawarin da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi wa shugaban na INEC, a lokacin da ya ziyarce shi.

Ya ce yawancin ayyukan da INEC za ta biya ma’aikata duk tura masu a asusun ajiyar su za ta yi.

Da ya ke magana kan ƙalubalen tsaro, ya ce wannan aikin jami’an tsaron ƙasa ne, kuma sun yi alkawarin babu wani gagararren da za’a bari ya haifar wa zaɓen 2023 da cikas.

Ya ce Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Ƙasa da ke ƙarƙashin Tsohon Shugaban Ƙasa, Abdulsalami Abubakar, shi ne zai shirya taron rattaba hannun amincewar da ‘yan takarar za su yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023, a cibiyar ICC a Abuja.

Ya ce INEC ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2023 a cikin kwanciyar hankali.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
Labarai

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Majalisar Dattawa
Labarai

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Labarai

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Next Post
Sauyin Kudi: Gwamnonin APC Sun Bukaci Buhari Da CBN Su Mutunta Umarnin Kotun Koli

Sauyin Kudi: Gwamnonin APC Sun Bukaci Buhari Da CBN Su Mutunta Umarnin Kotun Koli

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.