Hukumar zabe ta kasa INEC ta mayar da martani kan wani faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da ya nuna ana birne katukan zabe a cikin magudanar ruwa a jihar Ribas.
A cewar hukumar, ana zargin cewa a gidan wani babban dan siyasa ne a jihar aka bankado katukan na jefa kuri’a.
- Zaben Osun: Yadda Mawaki Portable Ya Sha Suka Kan Goyon Bayan APC
- IPOB Ta Yi Barazana Ga Jakadiyar Birtaniya A Nijeriya
Sai dai, a rahotannin farko, katukan na zaben an bankado su ne a jihar Imo, inda a martanin da kwamishina kuma shugaban wayar da kan masu jefa kuri’a da ilimantar da su na INEC, Festus Okoye, ya yi ya bayyana cewa, a binciken farko da aka yi kan maganar ya nuna cewa, an bankado katukan ne a jihar Ribas ,
Okoye wanda ya sanar da hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise da ke Abuja, a yau Juma’a’.
“Kalubalen da muka fuskanta da farko shi ne na kasa gano inda abin ya auku, inda ya kara da cewa, wasu sun ce ya auku ne a jihar Imo wasu kuma sun ce, ya auku ne a jihar Ribas .
“Amma bayan mun kai rahoto ga jami’an tsaro, sun gano cewa abin ya auku ne a jihar Ribas.”
Hukumar ta fara gudanar da cikakken bincike kan zargin wanda da zarar an gama binciken za ta sanar kan abin da ake ciki.