Bayan bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta bai wa Tinubu takardar shaidar lashe zabe da misalin karfe 3:00 na yamma.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan da sanyin safiyar Larabar nan, ya ce za a ba wa Tinubu da mataimakin shugaban kasa takardar shaidar cin zabe a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.
- Shugaban Faransa Zai Yi Ziyarar Kwanaki 5 A Afrika
- Gwamna Inuwa Ya Yi Jimamin Rasuwar Wakilin RFI, Shehu Saulawa
Mahmood ya bayyana cewa Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zo na biyu da 6,984,520, sai dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya zo na uku da 6,101,533, sai Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) wanda ya samu kuri’u 1,496,687 yayin zaben.
Shugaban na INEC ya bayyana cewa doka ta tanadar da a bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC takardar shaidar cin zabe bayan ya cika sharuddan doka a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sakamakon tattara zaben shugaban kasar da aka kwashe kwanaki hudu ana yi ya nuna cewa jimillar kuri’u masu inganci sun kai 24,250,940 wadanda aka kada.