Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa mai yiwuwa a satin farko na watan Fabrairu, 2024 za ta gudanar da ragowar zaɓuɓɓukan da za a sake da kuma na cike gurabu a wasu mazaɓu, yankuna da shiyyoyin tarayya da jihohi.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a taron da INEC ta yi da jam’iyyun siyasa a ranar Litinin, a Abuja.
- Manyan Hafsoshin Sojan Nijeriya Sama Da 113 Sun Yi Ritaya Daga Aikin Soja
- Wani Mutum Ya Halaka Sakataren Kotu Har Lahira A Jihar Adamawa
Yakubu ya ce, INEC ta ɗaura aniyar gudanar da zaɓuɓɓukan biyu – zaɓukan da za a sake da kuma waɗanda ba a samu gudanarwa ba duk a rana ɗaya.
“Abin da ya rage shi ne hukumar zaɓe ta gudanar da zaɓuɓɓukan da kotuna suka bada umarnin a sake a wuraren da za a sake zaɓuɓɓukan.
“Kamar yadda ku ka sani, shi zaɓe na ‘re-run’, zaɓe ne da ya ƙunshi jam’iyyu da ‘yan takara waɗanda suka rigaya suka fafata a babban zaɓe. Sai fa idan jam’iyya na buƙatar musanya ɗan takara idan ya rasu kafin a sake wannan zaɓen da za a yi.
“Shi kuma ‘bye-election’, zaɓe ne sabo da za a yi. Don haka, a wannan tsari, tilas ne jam’iyyu su sake gudanar da zaɓen fidda gwanaye cikin ƙa’idar kwanakin da dokar zaɓe ta gindaya.
“Zuwa yanzu dai Kotunan Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe sun umarci INEC ta gudanar da zaɓuɓɓuka a mazaɓu 34 da suka ƙunshi shiyyar sanata ɗaya, sai mazaɓun ɗan majalisar tarayya guda 11 da majalisun jihohi 22.
“Sai dai kuma daga zaɓuɓɓuka 34 ɗin da za a sake, wurare uku ne kawai za a sake zaɓen baki ɗaya.”
A ƙarshe Yakubu ya ce sai bayan an kammala sauraren shari’un zaɓen gwamnoni a Kotun Ƙoli, sannan INEC za ta tattara yawan shari’un da aka gudanar, domin yin bayanin su dalla-dalla.