Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ce za ta gurfanar da wasu da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi zaben 2023 a gaban kotu.
Hukumar ta ce mutanen da za ta gurfanar kan irin wadannan laifuka sun kai 215 daga bangarori daban-daban.
- Masarautar Zazzau Ta Dakatar Da Marafan Yamman Zazzau Kan Daukar Doka A Hannunsa
- Mutanen Da Ke Aiki A Karkashina Na Da Gidaje A Kasashen Waje, Amma Ba Ni Da Gida A Waje -Dangote
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne, ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga daukacin kwamishinonin zabe a babban ofishin hukumar da ke Abuja a ranar Talata.
Ya kara da cewa hukumar zabe za ta hada hannu da kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) wadda a cewarsa a shirye ta ke ta gurfanar da masu laifin a gaban kotu ba tare da an biya komai ba.
“Dole ne mu yarda cewa akwai wasu kalubale wasu na rashin kayan aiki, wasu na rashin isassun ma’aikata. Muna duba bayanan wadanda suka aikata laifuka,” in ji Yakubu.
“Akwai kararraki 215 daga ‘yansanda kan laifukan zabe, muna aiki tare da NBA don gurfanar da masu laifi. Tuni NBA ta gabatar da jerin sunayen lauyoyi 427 wadanda a shirye suke su gurfanar da wadancan kararrakin kyauta.”
Da yake nazarin zabukan, Yakubu ya ce zabukan 2023 sun samu kyakkyawan sakamako idan aka kwatanta da zabukan da aka gudanar a baya.