Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kai ziyarar ba-zata a sabon ginin Sashen koyar da Kwararrun likitoci da aka kammala a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe, da ke Damaturu.
Gwamnan ya kai wannan ziyarar ne domin gani da ido tare da tantance ingancin aikin da aka gudanar a cikin wannan babban asibitin.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababbun Shugabannin Gabon Da Ecuador
- Hisbah A Katsina Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Budurwa A Wani Faifan Bidiyo
Ziyarar ta zo ne jim kadan bayan da Kwalejin Horas da Kwararrun Likitoci ta Afrika ta Yamma (WACP) ta bayar da shaidar amincewa wajen hiras da manya da kananan likitoci 25, wanda cibiyar ta nema.
Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.
A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp