Uwargida ko kin san abin da za ki sa wa gashinki ya yi tsawo da laushi ya kuma magance amosani.?
Assalamu Alaikum masu karatu barkammu da sake saduwa da ku a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado da Kwalliya.
Ga Abubuwan da ya kamata Uwargida ki tanada; Yana da kyau sosai, sannan kuma yana gyara gashi ya sa shi laushi ya yi tsayi sannan kuma ya yi baki.
Da fari sai ki nemo bawon albasa, man albasa, man hulba, Neskef, man da habbatussauda:
Ga kuma yadda za ki hada shi:
Da farko za ki samu bawon albasa, albasa dai wadda muke amfani da ita to bawo na baya wanda muke zubar da shi daga yanzu karki sake zubar da shi ga amfanin sa ya zo, sai ki samu fry pan ki zuba wannan bawon albasar a ciki sai ki dora shi a wuta amma ki rage wutar saboda kar ya kone sai ki rika juya shi sama-sama har ya yi baki shi ne ya soyu idan ya yi baki sannan ki sauke shi ya dan huce, daga nan ki samu turminki mai kyau ki daka shi ya yi laushi, sai ki samu abin zubawa ki zube shi sannan ki kawo man albasa ki zuba sai man hulba shima ki zuba, sannan man habbatussaudah shima ki zuba, sai Neskef dinki shima za ki iya daka shi ko nika shi saboda ya yi laushi.
Bayan kin daka sai ki zuba shi a cikin wannan hadin sannan ki juya shi sosai ki gauraye shi, sai ki maida shi man kitson ki za ki ga abin mamaki in sha Allahu kanki zai yi laushi gashin ya yi tsayi sannan idan kina da amosanin kai zai miki maganin sa, sannan kuma fatar kanki za ta yi haske.