Hukumar kwallon kafar Ingila (FA) ta sanar da ta kawo karshen farautar da ta ke yi na sabon kocin babbar tawagar kwallon kafar ta maza ta kasar Ingila.
An tabbatar da Thomas Tuchel a hukumance a matsayin sabon koci, inda aka bayyana Anthony Barry a matsayin mataimakinsa.
Ana sa ran Bajamushen zai ja ragamar tawagar domin lashe manyan kofuna.
Thomas Tuchel ya jagoranci manyan kungiyoyin kwallon kafa kama daga Borrusia Dortmund, PSG, Chelsea da kuma kungiyarsa ta karshe Bayern Munich, inda ya lashe kofin Bundesliga.
Tun bayan rashin nasara da kasar Ingila ta yi a wasan karshe na European Cup a hannun kasar Spain ne tsohon kocin tawagar, Gareth Southgate, ya bayyana matakin ajiye aikinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp