Kasar Ingila ta sanar da matakin da ta dauka na rage haraji kan kayayyakin da ake shigar mata daga kasar Nijeriya sama 3,000, a karkashin wani shiri bunkasa kasuwancin kasashe masu tasowa (DCTC).
Jakadar kasar Ingila a Nijeriya, Richard Montgomery, shi ne ya shaida hakan a Abuja ranar Talata a wajen wani taron kara wa juna sani kan shirin Ingila na bunkasa harkokin kasuwancin kasashe masu tasowa da aka shirya da hadin guiwar ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci, cinikayya da zuba jari ta Nijeriya da kuma hukumar bunkasa fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa kasashen waje (NEPC).
Jakadar wanda ya samun wakilcin mataimakiyarsa, Misis Gill Atkinson, ya ce sun dauki matakin ne domin kyautatawa da bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasar Ingila da kuma Nijeriya.
“Shiri bunkasa hada-hadar kasuwancin kasashe masu tasowa na amfanar da kasashe 46, daga cikinsu kasashe 31 duk suna Afrika, kuma kasar da za ta zama muhimmiya a wannan bangaren ita ce Nijeriya.
“Wannan sabon tsarin cinikayyar ya fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yuli, kuma shi ne tsari mafi inganci da ke saurin saukawawa da bunkasa hada-hadar kasuwanci ga kowace kasa a fadin duniya. Kasar Ingila ta himmatu wajen kyautata dangartakarta da Nijeriya mai dadadden tarihi kuma da yunkurin ganin kowani bangare a tsakaninsu ta amfana da wannan alakar.
“Nijeriya ce za ta fi kowace kasa morar sabon tsarin bunkasa hada-hadar kasuwanci na CTS. Domin kuwa an rage haraji ga kayayyakin Nijeriya sama da 3000 da ke nuni da kaso 99 cikin dari na kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa kasar Ingila,” in ji shi.
Tun da farko a jawabinta, babbar sakatariya a ma’aikatar cinikayya da zuba hannun jari a Nijeriya, Dakta Ebelyn Ngige, da ta samu wakilcin daraktan kasuwanci na ma’aikatar, Suleiman Audu, ta ce sabon tsarin zai yi matukar taimakawa wajen bunkasar kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa kasar.
Ta jinjina wa kasar Ingila bisa daukan wannan matakin, ta na mai cewa hakan zai kara kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.