Iran ta bayyana cewa ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila ta hanyar amfani makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙi.
A cikin wata sanarwa da dakarun juyin-juya-hali na kasar Iran (IRGC) suka fitar, sanarwar ta ce “An harba gwamman jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami zuwa ƙasar Isra’ila.
- Jinyar Wata 7: Babu Abin Da Zan Ce Ga Masoyana Sai Godiya -Malam Na Ta’ala
- Wacce Kungiya Ce Za Ta Iya Lashe Gasar Firimiya?
Dama dai an shiga fargaba kan yiwuwar ɓarkewar faɗa tsakanin ɓangarorin biyu wato Iran da Isra’ila tun bayan zargin da Isra’ilar da kai hari kan ofishin jakadancin Iran a Syria ranar daya ga watan Afrilu da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an Dakarun juyin-juya-hali na Iran, wadanda suka hada da janar-janar guda biyu da kuma wasu ‘yan kasar Syria shida.
Tun a wancan lokaci ne Iran ta yi gargadin cewa ‘Isra’ila za ta dandana kudarta’.
Sanarwar da Iran ta fitar ta kara da cewa harin na yammacin ranar Asabar martani ne kan “manyan laifukan da Isra’ila ta sha tafkawa” – ciki har da harin ranar daya ga watan Afrilu.
Bayanin ya ce an yi wa wannan hare-hare da Iran ta kaddamar taken “Operation True Promise” a Turance.
Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin haske kan yanayin harin ba, baya ga cewa kasar ta harba gwamman makamai zuwa cikin Isra’ila.