Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati kadai dake wakiltar kasar Sin.
Haka kuma kasancewar kasar Sin daya tilo a duk duniya, ita ce babbar manufar da kasashen duniya suka amince da ita, kana tushen siyasa na raya hulda tsakanin Sin da duk kasashen da suka kulla ko ma suke son kulla alaka da kasar Sin.
Kuma a maganar da ake, akwai kasashe sama da 100 a fadin duniya, wadanda suka amince tare da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta zahiri da kasashen duniya suka amince da ita.
Wasu rahotanni na cewa, wai mahukuntan Taiwan sun gabatar da jerin “bukatu hudu” game da shigar yankin cikin MDD tare da yin ikirarin cewa, za su gayyaci “abokan diflomasiyya” don mika wa babban sakataren MDD wasikar tare, da ke neman ya gyara kuskuren da MDD ta yi wa kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD.
Wannan tamkar mafarki ne ko wasa da hankalin da wasu daga kasashen yamma ke yiwa jagororin yankin na Taiwan.
Kowa ya san cewa, Taiwan ba kasa ba ce, wani bangare ne na kasar Sin. Kuma duk wani abun da ’yan aware da masu goya musu suke yi na neman jirkita gaskiya da ma neman tayar da hargitsi ko neman ballewa, ko kadan ba zai taba canja gaskiyar lamarin ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ne.
Don haka, yankin Taiwan ba shi da tushe, ko hujja ko iko na shiga Majalisar Dinkin Duniya ko wasu kungiyoyin kasa da kasa da ke bukatar kasa ta zama mai ’yanci kafin ta shiga.
Duk wanda ya san tarihi ya san cewa, bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan na kasar Sin daya ne. Kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Ko da yake bangarorin biyu sun dade suna adawa da juna a siyasance, amma hakan bai sa an taba raba ikon mallakar kasa da cikakken yankin kasar Sin ba. Wannan shi ne ainihin yanayin batun Taiwan.
Hasashen ko mafarkin da hukumomin DPP suka yi na shigar Taiwan cikin tsarin MDD, a hakika wani yunkuri ne na haifar da ra’ayi na karya game da kasar Sin a matsayin “kasar Sin kasashe biyu” ko “kasar Sin daya kuma Taiwan daya” da kuma kalubalantar tsarin kasa da kasa.
Ya kamata masu barci ko mafarki kan wannan gurguwar shawara, su farka, su kuma fahimci cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan wani bangaren na kasar Sin da ba za a taba raba shi ba. (Ibrahim Yaya)