• English
  • Business News
Thursday, August 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

by Sulaiman
4 weeks ago
in Labarai
0
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Isra’ila ta rusa dubban gidaje a Gaza tun bayan ficewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a watan Maris, kuma a makonnin da suka gabata ta sanya alamar rusau a garuruwa da kauyuka da dama wadanda a baya suke dauke da dubban mutane.

Hotunan tauraron dan’adam sun nuna yadda aka barnata wurare da dama kuma sojojin Isra’ila sun sanya alamar ikirarin cewa wuraren na “karkashin aikin sojinsu”.

Mafi yawan gidajen an sanya alamar rusau, kuma da dama daga ciki sun riga sun lalace, amma akwai wasu da suka rage a tsaye.

Hotunan da aka tantance sun nuna yadda hayaki ya turnuke, bayan sojojin Isra’ila sun kai hare-hare a manyan gine-gine da makarantu da sauran ababen more rayuwa.

Masana shari’a da dama sun bayyana wa BBC cewa akwai alamun Isra’ila ta aikata laifukan yaki idan aka yi la’akari da yarjejeniyar Geneba, wadda a ciki aka haramta wa kasar da ke mamaya barnata ababen more rayuwa.

Labarai Masu Nasaba

NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo

Nijeriya Ta Kori Ƙarin ‘Yan Ƙasashen Waje 51 Da Aka Ɗaure Bisa Laifin Ta’addanci Da Zamba A Intanet

Kakakin rundunar tsaron Isra’ila ya ce suna aiki tare da la’akari da dokokin duniya, inda ya ce Hamas na boye “makamai” a cikin fararen hula, sannan suna “rusa gine-gine ne kawai idan ta zama dole.”

An gani a zahiri yadda Rafah ya lalace a kusa da bakin iyakar Masar

A ‘yan makonnin da suka wuce, sojojin Isra’ila da ‘yan kwangilar rusau sun sanya alamar rusau a gidaje da dama

Nazarin masa irin su Corey Scher da Jamon Ban Den Hoek ya nuna cewa barnar da aka yi a Gaza tun daga watan Afrilu ya yi muni a yankin.

 

Akwai manyan motocin katafila jigbe a yankunan

A watan Yuli, ministan tsaron Isra’ila, Katz ya bayyana tsare-tsarensu na kafa abin da ya kira “birnin aikin ceto” a Rafah, inda za a fara da ajiye Falasdinawa 600,000 a sansanin.

Yunkurin na shan suka sosai. Tsohon firaministan kasar, Ehud Olmert ya shaida wa BBC cewa tsarin zai yi kama “kafa sansanin ajiye wadanda ba a so.”

Tel al-Sultan na cikin biranen da suka fi yawan mutane a yankin Rafah. Akwai tarin mutane kuma a garin ne asibitin kula da yara da marayu da yaran da aka tsinta suke rayuwa.

Hotunan tauraron dan’adam da ke nuna yadda hare-haren sojojin Isra’ila ya barnata yankin duk da akwai gomman gine-gine da suka tsira.

Zuwa ranar 13 ga Yuli, hare-haren sun riga sun munana, inda ake samun manyan gine-gine sun rufta baki daya. Asibitin na cikin ‘yan tsirarun gine-ginen da suka rage.|| Haka kuma an sanya alamar rusau a gine-ginen da ke kusa da garin Saudi – garin da ke dauke da babban masallaci da makarantu da dama.

Wani faifan bidiyo da aka tabbatar ya nuna wata tanka na tafiya a titin Rafah wasu ma’aikata kuma suna diga.

Haka kuma Isra’ila ta yi rusau a wasu sassan zirin wadanda suka tsira daga hare-haren farko.

Birnin Khuza’a da ya yi fice da noma, wanda ke da da nisan kilomita 1.5 (mil 0.9) daga bakin iyakar Isra’ila.

Kafin fara yakin, birnin na da mutum 11,000, kuma yana da kasar noma mai kyau da ake noma tumatir da fulawa.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta rusa gine-gine 1,200 a Khuza’a, wadanda ta yi zargin kadarorin “‘yanta’adda” ne da Hamas ke amfani da su.

An samu labarai irin haka a birnin Abasan al-Kabira, inda kusan mutum 27,000 ke rayuwa kafin yakin. Hotunan da aka dauka a 31 ga Mayu da 8 ga watan Yulin sun nuna yadda aka daidaita yankin a cikin kwana 38.

Isra’ila ta kirkiri “sansanonin tsaro” a tsakanin wasu yankunan Gaza, kuma ta lalata gine-gine da dama a tsakanin su. Wurin da ta kai farmaki na kusa-kusan nan shi ne gab da gabashin Khan Younis, ciki har da Khuza’a da Abasan al-Kabira.

Haka kuma tun farkon yakin, masana suke hasashen Isra’ila na yunkurin kafa “cibiyoyin tudun mun tsira” ta hanyar rusa gine-gine da ke gab da bakin iyakarta.

A Kizan Abu Rashwan – yankin da ya yi fice da noma mai nisan kusan kilomita 7 daga bakin iyakar Isra’ila – kusan kowane gini da ke tsaye an rusa shi daga ranar 17 ga Mayu.

Sashen BBC Berify ya gabatar da sakamakon bincikensa ga IDF ciki har da wuraren da ta rusa, inda aka bukaci ta yi bayani, amma ba ta yi ba.

“Kamar yadda aka sani ne, Hamas da sauran kungiyoyin ‘yanta’adda na boye makamai a cikin fararen hula,” in ji kakakin IDF. Sannan ya kara da cewa IDF na “ganowa tare da barnata kadarorin ‘yanta’adda da suke cikin gine-ginen ne.”

Lauyoyin kare hakkin dan’adam da dama da BBC Berify ta zanta da su sun ce akwai alamun Isra’ila ta aikata laifukan yaki.

Eitan Diamond – wani babban lauya da ke aiki a cibiyar agaji ta Diakonia International Humanitarian Law Centre da ke Jerusalem – ya ce akwai ‘yar hujja da ta kafe da shi a cikin yarjejeniyar Geneba ta hudu.

“Dokokin duniya sun haramta wadannan mamayar da barnata kadarorin fararen hula a lokacin yaki, sai dai idan ya matukar zama dole,” in ji Mr Diamond said.

“Amma barnata kadarori saboda kawai zargin yiwuwar za a yi amfani da su a gaba ba ya cikin uzurin da aka tsara a yarjejeniyar.”

Farfesa Janina Dill, darakta a cibiyar shari’a da yaki ta Odford Institute for Ethics, Law & Armed Conflict ta ce kasar da ta yi mamayar dole ta killace wani yankin domin kare wasu mutane – wadda ta ce ba zai yiwu a yi amfani da karfin soji ba.”

Amma wasu masanan sun kare rundunar IDF.

Gine-gine da dama da IDF ta rusa sun zama kufai, “in ji Farfesa Eitan Shamir, darakta a cibiyar BESA Center For Strategic Studies da ke Isra’ila kuma tsohon jami’i a ma’aikatar tsare-tsare. Ya bayyana wa BBC Berify cewa gine-gine sun barazana ga masu komawa garuruwan su saboda za su iya rushewa a kowane lokaci”.

Haka kuma Farfesa Shamir ya ce akwai rashin tsari.

“Wuraren sun zama na yaki,” in ji shi. “Ko da ma IDF ta mamaye wurin, da zarar Isra’ila ta janye, mayakan suna komawa su dasa bama-bamai ko su boye a ciki.”

Babu alamar janyewa a yunkurin na rusau. Kafofin watsa labarai na Isra’ila sun ce IDF ta dauko manyan katafila da ake kira D9 daga Amurka.

Kuma sashen BBC na BBC Berify ya gano gomman tallata guraban aiki da aka watsa a zaurukan Facebook na ‘yan Isra’ila da ake neman ma’aikata da za su yi aikin rusau a Gaza, wadanda aka rika yadawa tun a watan Mayu.

Wasu rubuce-rubucen sun bayyana wuraren da za a yi aikin a Gaza kamar “yankin Philadelphi” da “yankin Morag” – duk a karkarshin IDF.

Da BBC Berify ya tuntubi wani dan kwangila, sai ya ce, “ka je (wasu maganganu) da kai da Gaza.”

Wani masani – Adil Hakue na tsangayar shari’a ta Rutgers – ya yi hasashen rushe-rushen IDF ba za su rasa nasaba ba da yunkurin kafa “yankin soji” da za ta “mamaye daga baya” ba.

Wasu masana kuma sun ce rusau din share fage ne domin kafa “cibiyar agaji” a Rafah – Shugaban cibiyar nazarin tsaro da tsare-tsare ta Institute for Strategy and Security da ke Jerusalem – ya ce watakila suna so ne su tursasa wa Falasdina barin zirin baki daya.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya taba bayyana wa a baya a wani taro da ‘yan majalisa cikin sirri cewa IDF za ta rusa gine-gine ne domin ya zama Falasdina ba su da wurin komawa”.

Amma a wajen ‘yan Gaza, matsala cebabb.a.

Moataz Yousef Ahmed Al-Absi daga Tel al-Sultan ya ce an mayar da gidansa kufai.

“na koma gidan ne kimanin shekara biyu kafin a fara yakin, inda nake tsammanin zan cigaba da rayuwa. Amma yanzu ya zama kufai,” in ji shi.

“Na rasa komai, yanzu ban san yadda zan yi ba.”

 

Kungiyoyin agaji sun bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Kungiyoyi agaji fiye da dari sun yi gargadin yaduwar mummunar yunwa a Gaza, inda mutane fiye da miliyan biyu ba su iya samun abinci.

Kungiyoyin sun ce a halin da ake ciki yanzu hatta ma’aikatansu su na fama da karancin abinci a Gaza.

Kungiyoyin agajin da suka fitar da rahoton mawuyacin halin da mutane ke ciki a Gaza sun hada da kungiyar likitoci ta kasa da kasa, da Sabe the Children da kuma Odfam.

Sun ce ma’aikatansu ba su da wani zabi illa su shiga layin neman agajin abinci tare da al’umma Gaza, wani abu da ke sanya su shiga yanayin da za a iya harbe su, saboda kokarin nema wa iyalansu abinci.

Sun bukaci a samar da tsarin rabon kayan agaji a Gaza ta hannun hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Isra’ila ta amsa cewa an samu raguwa da gagarumin rinjaye kan yawan kayan agaji da Falasdinawa ke samu, amma ta musanta cewa akwai yunwa a yankin.

Dr Graeme Groom babban likitan kashi ne a asibitin London, wanda kuma ya yi aiki a Gaza a watan jiya.

Ya ce: ”A kullum abokan aiki na aiko mani sako domin sanar da ni cewa babu abinci. Kwanaki biyu da suka wuce, wani babban jami’in mu ya shaida mani cewa babu abinci, kuma ko kadan babu, sai ya ce ai babu komai, asali ma cikin matsananciyar yunwa suke.”

Wani rahoton da ma’aikatar lafiya ta Hamas ta fitar ya ce mutane fiye da 30 suka mutu saboda tsananain yunwa a kanaki uku, lamarin da Isra’ila ta ce farfaganda ce kawai.

Kungiyoyin sun bukaci a gagauta kawo karshen yakin domin samun damar shigar da wadataccen abinci ga al’ummar Gaza.

Mun Ciro Wannan Rahoto Daga BBC Hausa


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Next Post

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Related

NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo
Labarai

NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo

4 minutes ago
Nijeriya Ta Kori Ƙarin ‘Yan Ƙasashen Waje 51 Da Aka Ɗaure Bisa Laifin Ta’addanci Da Zamba A Intanet
Labarai

Nijeriya Ta Kori Ƙarin ‘Yan Ƙasashen Waje 51 Da Aka Ɗaure Bisa Laifin Ta’addanci Da Zamba A Intanet

3 hours ago
Mafi Ƙarancin Albashin ₦70,000 Ba Zai Iya Tsamo ‘Yan Nijeriya Daga Ƙangin Talauci Ba – Amurka
Manyan Labarai

Mafi Ƙarancin Albashin ₦70,000 Ba Zai Iya Tsamo ‘Yan Nijeriya Daga Ƙangin Talauci Ba – Amurka

4 hours ago
Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan 
Manyan Labarai

Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan 

8 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

19 hours ago
Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a 
Labarai

Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a 

21 hours ago
Next Post
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

LABARAI MASU NASABA

NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo

NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo

August 21, 2025
Kura Za Ta Ce Da Kare Maye

Kura Za Ta Ce Da Kare Maye

August 21, 2025
Nijeriya Ta Kori Ƙarin ‘Yan Ƙasashen Waje 51 Da Aka Ɗaure Bisa Laifin Ta’addanci Da Zamba A Intanet

Nijeriya Ta Kori Ƙarin ‘Yan Ƙasashen Waje 51 Da Aka Ɗaure Bisa Laifin Ta’addanci Da Zamba A Intanet

August 21, 2025
Mafi Ƙarancin Albashin ₦70,000 Ba Zai Iya Tsamo ‘Yan Nijeriya Daga Ƙangin Talauci Ba – Amurka

Mafi Ƙarancin Albashin ₦70,000 Ba Zai Iya Tsamo ‘Yan Nijeriya Daga Ƙangin Talauci Ba – Amurka

August 21, 2025
Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan 

Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan 

August 21, 2025
Boniface

Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface

August 20, 2025
Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe

Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe

August 20, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

August 20, 2025
Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa

Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa

August 20, 2025
Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabbin Makamai Yayin Faretin Soja Na Ranar 3 Ga Watan Satumba

Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabbin Makamai Yayin Faretin Soja Na Ranar 3 Ga Watan Satumba

August 20, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.