Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na tsawon kwana 60 da Hamas domin ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Trump ya bayyana hakan ne a daren ranar Talata a dandalin sada zumuntarss mai suna Truth Social.
- Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea
- David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
Ya ce Amurka za ta yi aiki tare da dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa a lokacin tsagaita wutar domin yarjejeniyar zaman lafiya.
A cewarsa, ƙasashen Qatar da Masar waɗanda suka daɗe suna ƙoƙarin kawo zaman lafiya za su gabatar da tayin ƙarshe na yarjejeniyar.
“Ina fatan Hamas za ta karɓi wannan tayin domin alherin Gabas ta Tsakiya,” in ji Trump.
“Ba za su samu tayin da ya fi wannan ba abu zai ƙara muni idan suka ƙi.”
Har yanzu babu martani daga jami’an Isra’ila kan iƙirarin Trump ba.
Tattaunawar neman tsagaita wuta ta tsaya cak tun watanni da suka gabata saboda rashin jituwa kan matakin da za a ɗauka bayan an daina faɗa.
Isra’ila tana son ta ci gaba da samun damar kai farmaki idan ta ga dama, amma Hamas tana so a daina faɗa gaba ɗaya.
Ana sa ran Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai kai ziyara fadar White House a mako mai zuwa.
Trump ya ce zai yi magana da Netanyahu domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin.
A farkon shekarar nan, wani ƙoƙari na tsagaita wuta ya rushe a watan Maris bayan Isra’ila ta kai wani farmaki ba tare da sanarwa ba a Gaza wanda rahotanni suka ce ya hallaka fiye da mutane 300.
Daga baya Netanyahu ya kare farmakin, inda ya bayyana cewa Hamas ta ƙi sakin fursunon Isra’ila da ke hannunta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp