Isra’ila ta yi luguden wuta a sassa da dama na Gaza, musamman a yayin da yaÆ™i ya yi Æ™amari a garin Rafah.Â
Wannan hari ya haifar da babbar damuwa da asarar rayuka a cikin al’ummar Gaza.
- Gwamnatin Kano Ta Musanta Bullar Cutar Kwalara A Jihar
- Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Lashi Takobin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
A wayewar garin yau, mayaƙan Houti sun yi iƙirarin cewa sun yi amfani da wani sabon makami mai linzami wajen kai hari kan jirgin ruwan MSC Sarah V a Tekun Arabiya.
Yahya Sarea, mai magana da yawun Æ™ungiyar, ya bayyana cewa harin “harin mun yi shi ne kan jirgin ruwan kuma a da tabbacin na Isra’ila ne.
Cibiyar ‘United Kingdom Maritime Trade Operations’ ta ba da rahoton cewa ma’aikatan jirgin ruwan suna cikin Æ™oshin lafiya, sannan jirgin ya nufi tashar da zai tsaya ta gaba.
Wannan labari ya kara jawo hankalin duniya kan yadda rikice-rikicen yankin ke shafar zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Arabiya.