Mayaƙan ISWAP sun kai hari sansanonin sojoji da ke garin Buni Gari a ƙaramar hukumar Gujba, a Jihar Yobe.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na daren ranar Juma’a, bayan kwanaki kaɗan da gwamnonin Arewa maso Gabas suka yi taro a Jihar Yobe kan tsaro, tattalin arziƙi.
- Amurka Ba Za Ta Cimma Nasara Ta Hanyar Yakin Cinikayya Ba
- Jami’ar Tarayya Ta FUGA Ta Kirkiro Da Injin Kyankyasar ‘Yan Tsaki
Wata majiya daga hukumomin tsaro ta tabbatar da wannan hari, inda ta ce maharan sun kai hari a wani ɓangare na sansanin sojoji a Buni Gari.
Garin Buni Gari yana da nisan kilomita bakwai daga Buni Yadi, inda ake horar da sojoji.
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa maharan sun fara harbi kan mai uwa da wabi kafin su ƙona kayayyakin sojoji da kuma gine-ginen al’ummar yankin.
Wakilinmu ya ce mayaƙan “Operation HADIN KAI” sun fafata da maharan lokacin da suka kai hari Buni Gari.
Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da faruwar lamarin a shafinta na sada zumunta da safiyar yau Asabar.
A cewarta, “Mayaƙan Operation HADIN KAI suna ci gaba da fafatawa da mayaƙan ISWAP a Buni Yadi.”
Rahotannin sirri sun bayyana cewa jami’an sojin sun samu taimako daga mafarauta da ƴan bijilanti kafin daga baya maharan su gudu.
Har yanzu, ba a san adadin asarar da aka yi ba sakamakon harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp