An sako Babban Daraktan Lafiya na Babban Asibitin Gubio, Jihar Borno, Dakta Geidam Bulama, wanda ISWAP ta yi garkuwa da shi a watan Maris 2022.
An sace Bulama ne a shekarar da ta gabata, lokacin da ISWAP ta kai hari a karamar hukumar Gubio da ke da tazarar kilomita 70 daga birnin Maiduguri.
Kafin a yi garkuwa da shi, Bulama shi ne likita daya tilo da ke kula da daukacin karamar hukumar Gubio.
A cewar Zagazola Makama, wani masani kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, a lokacin da aka yi garkuwa da Bulama, maharan sun yi wa matarsa alkawarin cewa ba za su kashe shi ba.
Majiyoyi sun ce, ISWAP sun kai Bulama da sauran mutanen da suka sace zuwa gabar tafkin Chadi inda suke tilasta masa yin jinyar mayakan da suka jikkata da iyalansu na tsawon watanni.
Wata majiya ta ce kokarin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ne ya sa aka sako Dakta Bulama.