ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta

by Idris Aliyu Daudawa
9 months ago
Hutu

A garin Nyanya, da yake ƙarƙashin Babban Birnin Tarayya Abuja, matar aure, Hauwa Moji, ita ma ta bada labarin irin yadda suke fuskantar lamarin. Ta bayyana cewa ‘ya’yanta b za su ci gaba da karatu ba a wannan zangon ba, domin komai ba sai saboda an ƙara kuɗin haya da kuma na makaranta, tace irin wannan lamarin da zai laƙume kuɗaɗe masu yawa mijinta ba zai iya ɗaukar nauyin abubuwan ba a lokaci ɗaya.

Ta ce, “Matsalar ta fara ne bayan da minjinta ya rasa aikin koyarwa da yake yi ya fara neman wani. Cikin ikon Allah sai ya samu wani amma kafin a daga hutu. Wani abin takaici dole ne ya fita daga gidan da aka ba shi makarantar da ya ajiye aiki, hakan ya nuna dole ne ya nemi wani wurin zama.

“Ta ci gaba da bayanin mijina daga ƙarshe ya samu wuri a Nyanya. Maigidan yace zai biya Naira 400, 000, amma saboda baya kusa, sai mai bada hayar ya ce, bayan ya amshi wasu ƙarin kuɗi, sai ya tsaya kai da fata cewa dole ne sai ya biya Naira 700, 000 a shekara ta farko saboda akwai kuɗin da ake ba mai bada haya, kuɗin Lauya, da kuma sauran wasu kuɗaɗe daban, daga nan kuma shekara mai zuwa sai ya biya, Naira 400,000 .

ADVERTISEMENT
  • Hukumar SUBEB Ta Yi Kira Ga Al’umma Da Su Sa ‘Ya’yansu Makaranta
  • ‘Yan Makaranta Sun Kera Mota Mai Amfani Da Lantarki A Sakkwato

“Bai da zaɓi dole ya haɗa ya biya da kuɗaɗen da yara ya kamata a biya ma su kuɗin makaranta, maimakon haka sai ya biya kuɗinhaya suka shiga cikin gidan. Ta ci gaba da ƙarin bayani.Bamu da abinda ya dace mu yi wanda fi wanda muka yi, amma ba maganar fara karatun yara ba a wannan zangon, sai kuma lokacin da abubuwa suka fara gyaruwa su ci gaba da karatu.

Ita kuma Gloria Oche, da take da ‘ya’ya uku ya bayyanawa LEADERSHIP cewa ‘yar’uwarta tana tunanin ko za ta ɗauki mataki da ta san zai fishshe ta.

LABARAI MASU NASABA

PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar Jamiyyar

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki.

“Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.”

A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta, da kuma sauran abubuwa.

“Idan aka dukkan ƙarurrukan da aka yi abin zai zama da akwai ɗaure kai. Kuɗin haya ya ƙaru a wannan unguwa idan kuma mutum ya yi bincike kuma za a gane irin mutanen da suke zama a wurin, waɗanda abinda suke samu ba kasafai yake biya masu buƙata ba. Don haka idan har ka sa ɗanka wannan makaranta,duk da yake dai z aka, iya biya,amma idan wani babban abu ya taso kamar kiuɗin haya abin sai dai ayi shiru kamar yadda ya ce,”.

Wani mahaifi, Joseph Hange wanda ‘yarsa take zuwa makarantar Bright Child Academy, Lugbe, cewa ya yi sabuwar shekarar karatun ta zo da abubuwa masu sosai zuciya.

“Abin bai tsaya kan maganar ƙare-ƙaren kuɗaɗen bane kawai na kuɗin makaranta, abinci, Littattafai, suturar zuwa makaranta, ziyarar buɗe ido, duk a haɗa su wuri ɗaya. Kamar su da suke harkar kasuwanci, lamarin tattalin arzikin ba shi da daɗi.Cewa ya yi sun tattauna a gida ko daga ƙarshe irin wannan tafiyar za ta ɗore”.

Yayin da Iyaye lamarin ya hana su kwanciyar hankali,su ma Malaman makarantar kamar duk jirgi ɗaya ya ɗauko su.Domin kuwa yawancin makarantu yawan ƙarin kuɗin makaranta bai kai wag a ƙarin albashi ga su Malaman makarantar.

Wani Malami mai suna Moses Sachi a Abuja shi ma abin ya dame shi, saboda kuwa cewa yayi “Muna dai jin Iyaye suna kokawa, amma mu ma a matsayinmu na Malamai, matsalar da take damun Iyayen yaran muma ita ce ke damun mu .Lamarin kuɗin haya, abinci, da zirga- zirga abin yana ci mana tuwo a ƙwarya.

Wasu daga cikinmu akwai ayyukan da muke yi domin a samu tsira da mutunci kamar, zuwa koyar da darussa a gida, ƙananan sana’oi, kawai saboda dai mu samu kulawa da Iyali . Wasu makarantu sun ɗan yi ƙarin albashi wanda bai maganin matsin tattalin arzikin da kowa yake fuskanta ba, bama kamar talaka kamar yadda ya jaddada” .

Binciken da LEADERSHIP ta yi rahoton ya nuna matslar ba kawai ta ƙare bane kan ƙarin kuɗin makaranta ba.Kuɗaɗen haya sun ƙaru a sassa daban daban kamar su Abuja, Legas, da kuma wasu manyan wurare kamar Karu, Lugbe, da Gwarimpa da sauarn sassan Babban Birnin Tarayya Abuja, masu gidaje sun ƙara kuɗin haya da kashi 30 kamar yadda binciken ya nuna

Shi yasa Iyayen da suke biyan kuɗin makaranta dubban Nairori yanzu dole ne su san irin hanyar da za su bi, domin su nemi ƙarin kuɗin da za su cika domin biyan haya.

Wani mahaifi a Nyanya, mai suna Isaac Terseer, ya yi lamarin kallon abinda zai yi wuyar jurewa:

Inda ya ce “Wannan tamkar mutum ya riƙa bin inuwa ne da ƙoƙarin kamata.An ƙara kuɗin makaranta, kuɗin haya sun ƙaru.

Wannan halin ƙuncin rayuwa tana sa mutane ko iyalai su cikin halin ni’yasu kan yadda za su yanke shawarar daga cikin abubuwan da suka kamata su yi su ɗauki ɗaya da suke ma kallpon ya fi muhimmanci. Wasu na canza wa ‘ya’yansu makaranta zuwa wadda kuɗin da za su iya biya.Wasu suna tunanin yanke shawarar a riƙa koya masu a gida, ko kuma maida su makarantun gwamnati duk kuwa da yake akwai matsalar kayan aiki da, da rashin nagartar koyarwar.

An samu bayanan da suke nuna Iyaye na biyan tsakanin Naira milyan 3 zuwa 5 kowane zangon karatu.

Ta ɓangaren tsaka- tsaki ana biyan Naiar 800,000 zuwa milyan 2.5 kowane zangon karatu.

Waɗanda ake ma kallon masu sassauci ne a Abuja ana biyan Naira 120,000 zuwa 200, 000 a kowane zangon karatu.

Hutu
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

MASU ALAKA

PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar  Jamiyyar
Manyan Labarai

PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar Jamiyyar

June 21, 2026
An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi
Manyan Labarai

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

June 21, 2026
Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni
Manyan Labarai

Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni

June 21, 2026
Next Post
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

'Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

June 22, 2026

Mutane 842 Ne Suka Rasa Ransu, Aka Yi Garkuwa Da Sama Da 270 A Watan Mayu – Rahoto

June 21, 2026
PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar  Jamiyyar

PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar Jamiyyar

June 21, 2026
An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

June 21, 2026
An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 21, 2026
Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

June 21, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam

Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam

June 21, 2026
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

June 21, 2026
Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

June 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.