An kashe akalla jami’ai hudu na rundunar hadin gwiwa ta farar hula (CJTF) da ma’aikata hudu da ke aiki a Ma’aikatar Gine-gine, Gyara da Matsugunni ta Jihar Borno (RRR) a wani sabon hari mai muni da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka kai a garin Mayenti da ke karamar hukumar Bama a jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, harin ya faru ne a ranar Litinin, sa’o’i bayan da Babban Hafsan Sojan Sama (CAS), Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya ziyarci Maiduguri a rangadin aikinsa na farko zuwa sansanin ayyukan yaki da ta’addanci na a arewa maso gabas na rundunar sajin sama.
An kashe sojoji biyu da jami’ai biyu na CJTF a ranar Juma’a lokacin da ‘yan ta’addan suka yi wa sojojin rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation Hadin Kai’ kwanton ɓauna a wani sintiri da rundunar ke yi a kullum a Wajiroko da ke Azir Multe a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Mayenti, inda harin ya faru, yana da nisan kilomita kaɗan daga Darajamal da ke Bama inda ‘yan ta’addan, watanni da suka gabata, suka kashe mutane sama da 60, ciki har da sojoji biyar tare da kone gidaje da dama.
Majiyoyin leƙen asiri masu inganci sun ce ‘yan ta’addan sun kai hari kan al’umma da babura da motocin yaƙi a wani yunƙuri na mamaye sansanin sojojin da ke wurin.
Majiyoyin sun ce, duk da cewa sojoji sun yi nasarar dakile maharan, amma artabun ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro huɗu na sa kai waɗanda ke gadin garin.
Haka kuma, an ruwaito cewa sojoji huɗu sun ɓace a lokacin harin, kuma har yanzu ba a san inda suke ba.
‘Yan ta’addan, yayin da suke guduwa da gawarwakin mayakansu a cewar majiyar, sun ƙone manyan motoci biyu mallakar Ma’aikatar RRR, sannan suka kashe ma’aikata huɗu da ke aiki a yankin.














