Mayakan ISWAP sun kai farmaki tare da sace wasu ma’aikatan agaji a Karamar Hukumar Monguno a Jihar Borno.
Kazalika, sun kashe jami’an tsarom hadin guiwa na JTF a ranar Juma’a.
- Ya fada rijiya yayin da ya ke kokarin jefa mai masa aiki don yin tsafi da shi
- 2023: Muna tattaunawa da Peter Obi kan yiwuwar hada takararmu — Kwankwaso
Wannan ma dauke ne cikin wani rahoto da Zagazola Makama, masani kan harkar tsaro da ke yankin Chadi, ya bayyana wa wakilinmu cewar mayakan na ISWAP sun kai harin da misalin karfe 9 na daren ranar Juma’a.
A rawaito cewar mayakan sun shiga garin ne ta garin Marte da ke Karamar Hukumar Marte, sannan suka bi ta Gana Ari.
Daga bisani kuma suka shiga kai tsaye gidan ma’aikatan agajin da harbi kan mai uwa da wabi.
Majiyar ta ce sun yi kokarin satar motoci guda uku a gidan amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, wanda daga bisani suka yi awon gaba da ma’aikatan agajin.
Har wa yau majiyar ta ce sun garzaya ofishin Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA), sannan suka sace wata motar kirar Hilux tare da kashe jami’an tsaron hadin guiwa ma JTF sannan suka raunata mutum daya.