Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Fulham, Alex Iwobi, na dab da kafa sabon tarihi a gasar Firimiya a matsayin ɗan wasan Nijeriya da ya fi buga wasanni a tarihin gasar. Idan Iwobi ya buga wasan da Fulham za ta kara da Arsenal a filin Craven Cottage yau Asabar, zai zama ɗan wasan Nijeriya na farko da ya kai buga wasanni 299 a Firimiya.
A halin yanzu, Iwobi ya buga wasanni 298, inda yake daidai da tsohon ɗan wasan Newcastle United, Shola Ameobi, wanda ya riƙe wannan tarihin tsawon lokaci. Wannan zai kasance babbar nasara ga Iwobi wanda ke da shekaru 29 a duniya, tun da ya fara wasansa na farko a Firimiya ranar 27 ga watan Oktoba, lokacin da Arsenal ta fafata da Swansea City.
Iwobi, wanda ya fara wasansa a Arsenal, ya taka leda a ƙungiyoyin uku a gasar Firimiya — Arsenal, Everton, da kuma Fulham inda yake bugawa yanzu. A duk waɗannan ƙungiyoyi, ya zama ginshikin tawaga saboda bajintarsa da ƙwazo a fili.
Tun bayan zuwansa Fulham, Iwobi ya tabbatar da matsayin sa a ƙungiyar, yana taimakawa wajen inganta tsarin wasan ƙungiyar. Idan ya buga wasan yau, zai kafa tarihi a matsayin ɗan wasan Nijeriya da yafi taka leda a gasar Firimiya tun fara gasar a shekarar 1992.