ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jabun Kayayyaki Sun Mamaye Kasuwannin Nijeriya

by Ra'ayinmu
10 months ago
Mamaye

Ba karamar damuwa ce, musamman ma ga masu kishin Nijeriya,idan aka yi la’akari da sanarwar da hukumar  kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta yi na cewar, ta lalata jabun Magununa da kudinsu ya kai  sama da Naira biliyan 120, a cikin watannin shida da suka gabata kacal.

Wannan adadin, ya kai na yawan jabun magungunan da Hukumar ta kwace ne daga watannin Oktoba zuwa Disamba na 2024.

  • Fashewar Bam Ya Kashe Dalibi ɗaya, Ya Jikkata 4 Abuja
  • Sukar Gwamnatin Tinubu: Haƙiƙanin Gaskiyar Kama Obi A Abuja

Adadin, ya jefa matukar fargaba a zukatan al’ummar kasa da ke yin amfani da magungunan wajen nemawa kansu lafiya, musamman ma  irin wannan dimbin magungunan na jabun da ake shigowa da su cikin Nijeriya, aka kuma wucewa da su, kai tsaye, zuwa kasuwannin kasar domin sayarwa jama’a.

ADVERTISEMENT

Hakan ya kara fallasa yadda yanayin iyakokin kasar suka kasance a matsayin kara zube wajen shigo da nau’oin jabun kaya cikin kasar, ba tare da sa idon masu kula da iyakokin kamar yadda ya kamata ba.

Kazalika ma, kwace irin wadannan jabun kayan, da bata garin masu sayar da magungunan na jabu ke yi domin samun kazamar riba, hakan na kuma kara jefa marasa lafiyar, a cikin wani mummunan yanayi na rashin lafiyar da suke fuskanta.

LABARAI MASU NASABA

Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule

Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna

A samamen da Hukumar ta kai a manyan Shagunan sayar da jabun magungunan da ke a kamar Legas, Fatakwal, Abiya da kuma Abuja, ta bankado irin wadannan jabun magungunan da kudinsu ya kai na sama da biliyoyin Naira.

Wannan matsalar, tana kara haifar da kalubale ga tsarin kiwon lafiyar kasar da kuma fannin tattalin arziki.

Bugu da kari, Hukumar ta kuma bankado jabun lemon Kwalba a wajen baje kolin kaya da ke  jihar Legas, tare da kuma  garkame wasu masana’antun da suke sarrafa Shinkafar da ta lalace da kudinta ya kai kimanin Naira biliyan biyar a jihar Nasarawa, wanda hakan ya nuna irin babbar ta’asar da masu son kazamar ribar, suke aikatawa.

Wannan gano jabun kayan, ya zo daidai da lokacin da ake yin nazari kan yawan kudaden da marasa lafiya suka kashe, wajen sayen magunguna.

Shugabar Hukumar ta kasa Farfesa Mojisola Adeyeye ta alakanta irin wadannan masu sayar da jabun magungunan domin samun kazamar riba, a matsayin makasa.

Hukumar ta kuma kulle manyan Shaguna 150 a kasuwar Eziukwu, da ke a yankin Aba da ake sayar da jabun Lemon Kwalba.

Kazalika ma, sayar da irin wannan jabun kayan yana hanawa Gwamnati samun kudaden shiga, tare da kuma da zubar da mutuncin Nijeriya, a idon kasuwar duniya, inda kuma a yayin da irin wadannan jabun magungunan suka cike kasuwa, ke haifar da gasa a tsakanin ainihin masu sarrafa magungunan na gaske, tare da haifar masu da asara da durkushewar kasuwancinsu.

Bisa ga namu ra’ayin, a yayin da hukumar NAFDAC ke kara jajircewa wajen yakar irin wadancan mutanen masu sarrafa jabun magungunan, ta canci yabo.

Yadda aka lalata jabun kayan da kudinsu su ka kai na kimanin Naira biliyan 120, hakan ya nuna cewa, akwai gazawa ta magance matsalar.

Kazalika, hakan ya janyo bijero da tambaya a zukatan ‘yan Nijeriya, na rashin sa ido a iyakokin kasar.

Ya zama wajibi ne a dauki matakai daban daban domin kawo karshen ita wannan matsalar.

daya daga cikin matakan, na farko, ya kamata a kulla hadaka mai karfi a tsakanin NAFDAC da jami’an Hukumar Kwastam da kuma sauran Hukumomin tsaro, don a dakile shigo da jabun kaya cikin kasar.

Abu na biyu kuma shi ne, a rinka hukunta su batagarin da suke sarrafa kayan jabun, don hakan ya zama darasi ga sauran masu tunanin aikata  irin haka a nan gaba.

Kuma ya kamata a rinka yin amfani da kimiyyar zamani wajen dakile shigo da kayan na jabu da kuma samar da na’urorin zamani, da za su rinka tantance, kayan da ake shigowa da su.

Kazalika ma, ya zama wajbi, Hukumar NAFDAC, ta kara kaimi wajen ilimantarwa da fadakar da ‘yan kasar kan sayen kaya masu inganci,don  haka akwai bukatar a samar da shirye-shiyen ilmantarwa a makarantu da hakanan  a cikin al’umomi, kan yadda za a iya saurin gane jabun kaya a kuma  kai rahoto, ga mahukuntan kasar nan.

Akwai matukar bukatar sahihan kamfanoni masu zaman kansu da masu saye da sayarwa, suma su kara jan damara, wajen yakar masu sarrafa kayan jabu, musamman ma ta hanyar yin amfani da kimiyyar zamani, don gano jabun kaya.

Ya kuma kamata su rika yin aiki kafada – kafada da Hukumomi a kasar nan, domin kare kayan da suke sarrafawa da kuma kare lafiyar, masu sayen kayan domin su yi amfani da su.

Idan har ba a kawo karshen wadannan matsalolin da aka zayyana a sama ba, za ci gaba da komawa ‘yar gidan jiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule
Manyan Labarai

Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule

November 13, 2025
Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna
Labarai

Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna

November 12, 2025
Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 
Labarai

Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 12, 2025
Next Post
Ingancin Makarantu Masu Zaman Kansu Ya Tabarbare

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

November 12, 2025
Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 12, 2025
Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

November 12, 2025
Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

November 12, 2025
'yansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi

November 12, 2025
Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci

Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci

November 12, 2025
Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki

Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki

November 12, 2025
Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista

Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista

November 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.