Shugaban haɗin gwiwar Arewa maso Yammacin jam’iyyar ADC, Hon. Abdullahi Umar, ya ƙaryata zargin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Dumebi Kachikwu, ya yi cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mamaye jam’iyyar.
Umar ya kira maganganun Kachikwu “ba su da tushe” tare da zargin cewa suna ƙoƙarin ɓata sunan shugabancin jam’iyyar.
- Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
- Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe
Ya bayyana cewa rikicin shugabanci a jam’iyyar ya riga ya ƙare, inda ya ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta amince da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, tare da Rauf Aregbesola a matsayin sakataren riƙon ƙwarya.
Umar ya zargi Kachikwu da yin ƙarya cewa shugabancin ya aikata jabun takardu, inda ya bayyana cewa ba shi da hujjar kai su kotu, shi ya sa yake yaɗa zarge-zarge marasa tushe.
Ya jaddada cewa ADC tana mayar da hankali kan gina siyasa mai tushe a ƙasa wadda za ta kare muradun talakawa.
Ya kuma zargin Kachikwu da abokan aikinsa da goyon bayan gwamnatin APC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp