Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce jagorori, da al’ummun Afirka, ciki har da na kasar Angola ne ke da ta cewa, game da ko kasar Sin na haifar da alherai a Afirka ko akasin hakan.
Wang Wenbin, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na Larabar nan, a matsayin martani ga kalaman wasu kafafen watsa labaran kasar Japan na baya bayan nan, yayin da suke zantawa da shugaban kasar Angola João Manuel Lourenço, lokacin da ya ziyarci Japan din.
Cikin tsokacin kafofin watsa labaran na Japan, an jiyo suna cewa wai Japan, na damuwa game da babban tasirin da kasar Sin ke yi a nahiyar Afirka. Sai dai a martanin da shi kan sa ya mayar, shugaba Lorenzo ya ce bai ga dalilin da zai sa Japan ta damu da harkokin da Sin ke gudanarwa a Afirka ba. Ya ce maimakon nuna yatsa, kamata ya yi ma dukkanin sassa su yi maraba da hadin gwiwar kasa da kasa, ba tare da mayar da wani bangare saniyar ware ba.
Game da hakan, Wang Wenbin ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, wadda ya ce alaka ce ta cin moriyar juna mai tattare da alherai. Kaza lika a matsayin ta na muhimmiyar abokiyar cudanya a Afirka, Angola ta zamo kasa ta 2 mafi girman cinikayya ta Sin a Afrika.
Daga nan sai Wang ya bayyana cewa, Afirka nahiya ce mai cike da karsashin cimma buruka, kuma kasashen nahiyar masu tarin yawa, na kan hanyar samun ci gaba da farfadowa, suna kuma bukatar kakkarfan tallafi da hadin gwiwa daga sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)