Daya daga cikin jaruman fina-finan da ludayinsu ke kan dawo Sadik Sani Sadik ya bayyana batutuwa game da rayuwarshi ta yau da kullum da kuma ta fim, inda ya ce bayan harkar fim ya na ware wani lokaci da yake motsa jiki musamman taka leda, don kamar yadda yace dole ne jarumin fim ya kasance ya na motsa jiki domin samun lsashshiyar lafiya da za ta taimaka mashi.
Sadik wanda ya kasance jarumin masana’antar Kannywood tsawon lokaci, ya yi waiwaye dangane da gwagwarmayar da yayi kafin ya zamo abinda ya zama a halin yanzu, inda ya ce daga cikin sana’oin da ya yi kafin yanzu akwai bunburutu, kwadago da sauran tallace-tallace domin kawai a rufawa kai asiri.
- Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (3)
- Nazarin CGTN: Kasar Sin Na Bayar Da Gudunmuwa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran
Harkar fim ta yi mani riga da wando saboda ta sanadinta na samu alherai da dama, wanda yanzu nafi karfin abubuwa da dama kama daga abin da zan ci, tufafin da zan saka, motar da zan hau da gidan da zan zauna duka na mallake su sakamakon wannan harka ta fim, haka ya sa nike matukar alfahari da ita in ji Sadik a wata hira da ya yi da DW Hausa.
Da yake amsa tambaya a kan yadda yake mayar da martani a matsayinsa na jarumi a shafukan sada zumunta yayin da wasu su ka yi mashi abin da ya sosa mashi zuciya, jarumin ya ce galibi idan na dora wani abu a shafukana na sada zumunta ba lallai ba ne in koma kan abinda mutane ke fadi, muddin sakon da nike son in isar ya tafi inda nike bukata to shikenan bukata ta biya.
Akan burin da yake fatan cimma a rayuwa, jarumin dan asalin birnin Jos ta jahar Filato ya ce kowane dan adam yanada burika da yake son cimma kafin mutuwa, to amma shi dai ya cika wasu daga cikin burikansa na rayuwa duk da cewar zuwa gaba idan da hali ya na fatan watarana zai shiga siyasa har ma ya fito takarar gwamnan Jihar Filato.
Abinda ya sa nike fatan ganin na zama gwamna shi ne saboda banida wani burin da ya wuce in ga cewar matsalar tsaro ta kau a Nijeriya musamman Arewacin kasar inda wasu ke wasa da rayukan al’umma saboda wata bukata ta kashin kansu, wasu tsiraru na amfani da rayukan mutane a matsayin kasuwanci ko kuma don neman daukaka ya kara da cewa.
A ci gaba da hirar Sadik ya amsa tambayar da aka yi mashi a kan fina-finan da yayi da kuma wadanda yake kallo a matsayin wanda yafi so a cikinsu, inda ya ce daga cikin fina-finan da ya fito wadanda kuma yafi so, akwai Mati Da Lado sai kuma wani fim mai suna Dan Marayan Zaki.
Abinda ya sa nafi son wadannan fina finai shi ne ba don komai ba sai don kawai su na daya daga cikin ayyukan da nafi wahala kuma na kara samun gogewa a wannan sana’a tawa, hakazalika su ne fina-finan da aka fara sanina dasu kuma aka fara sanin wanene Sadik Sani Sadik da kuma abinda zan iya yi idan aka dora mani kyamara.
Daga karshe Sadik ya bayyana sirrin samun daukakarshi a masana’antar Kannywood, da cewa ba komai bane ya sa ya samu daukaka illa addu’ar iyaye da kuma jajircewa saboda na dauki harkar fim a matsayin babbar sana’ar da na dogara da ita yanzu, kuma nike rufawa kaina asiri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp