Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng, ya bayyana cewa, kasar Sin na matukar adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko na cinikayya, kuma za ta dauki kwararan matakai na maida martani a kan duk wani mataki da aka dauka a kanta.
Wanda ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin bude bikin ranar magungunan gargajiya ta kasar Sin a jiya Asabar, Xie ya yi kira da a kara nuna sha’awa da kwarin gwiwa a kan magungunan gargajiya na kasar Sin (TCM) dominn magance kalubalen da ake fuskanta a wannan zamanin.
- Har Yanzu Ruhin Taron Bandung Yana Tare Da Mu Wajen Kara Karya Lagon Babakere
- Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
Xie ya kara da cewa, wayewar kan kasar Sin tana ba da shawarar yadda za a inganta ci gaban duniya baki daya da kuma amfanar da kowane dan’adam mai rayuwa a doron kasa.
Ya kuma ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko yakin kasuwanci. Kuma wannan ba wai don kare muradu da martabar kasar Sin ba ce kawai, har ma da kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci.
A cewarsa, “Idan har wata kasa ta dage kan kakaba mana yakin haraji ko kuma yakin kasuwanci, to tabbas za mu yi gaba-da-gaba da ita ba tare da tsoro ba, kuma tabbas za mu dauki kwararan matakan mayar da martani.”(Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp