Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu.
Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A farkon shekarar bana kuma, memban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya kai ziyara Najeriya cikin nasara, hakan ya kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. A cewar jakadan, Sin tana son hada shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da manufar fatan samun farfadowa ta Najeriya, da kara hadin gwiwa bisa manufofin raya kasashen biyu, da raya manufar makomar bai daya ta Sin da Najeriya mai inganci, yana mai cewa, ta hakan za su taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a duniya.
A nata bangare, madam Bianca Odumegu-Ojukwu ta bayyana cewa, shugaba Tinubu ya kai ziyara kasar Sin a shekarar bara, lamarin da ya shaida cewa, Najeriya tana maida hankali ga raya dangantakar dake tsakaninta da Sin. Ta ce kasar Najeriya ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak, kuma tana son hada hannu da kasar Sin wajen aiwatar da ayyukan da aka cimma a ganawar shugabannin kasashen biyu da taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, ta yadda za a inganta hadin gwiwar kasashen biyu har ya amfanawa jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp