Kwamitin gudanarwar hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ya gudanar da taro na musamman game da batun kiwon lafiya a yankunan Falasdinu da aka mamaye.
Jakadan Sin dake ofishin Geneva na MDD, da sauran hukumomin kasa da kasa dake kasar Switzerland Chen Xu, ya gabatar da jawabi a yayin taron, inda ya bayyana matsayin kasar Sin, da kuma matakanta da ra’ayinta na kawo karshen tashin hankali.
- Xi Ya Bukaci A Tsagaita Bude Wuta Tare Da Gudanar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
- Jami’in Diflomasiyyar Falasdinu: PA Ta Godewa Kasar Sin Bisa Aikewa Da Agaji Ga ’Yan Gaza Cikin Sa’o’in Bukata
Chen Xu ya bayyana ra’ayoyinsa uku game da jigon taron. Na farko akwai batun inganta tsagaita bude wuta. Ya ce bangaren kasar Sin yana nuna damuwa game da dorewar yaki a zirin Gaza. Ya ce ya kamata bangarori masu alaka da hakan su kwantar da hankali, su ba da damar samun zaman lafiya, da baiwa jama’ar wurin zarafin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Kaza lika a cewar jami’in, bangaren Sin ya yi kira ga sassan kasa da kasa, musamman kasashen dake da tasiri kan batun Falasdinu da Isra’ila, da su ba da gudummawarsu ta sauke nauyi, ta inganta tsagaita wuta cikin dogon lokaci, kuma su kiyaye lafiya da ’yancin kasancewar fararen hula a yankin.
Na biyu, a warware matsalar kiwon lafiya. Ya ce kamata ya yi bangarori daban daban su yi iyakacin kokarin kiyaye tsaron likitoci da kayayyakin kiwon lafiya, su nuna goyon baya ga ayyukan WHO, da sauran hukumomin jin kai, da ba da magunguna, da kayayyakin aikin kiwon lafiya da ake bukata cikin gaggawa a yankin, da kuma ceto da kwashe wadanda suka jikkata. Ya ce ya kamata a yi hangen nesa, a taimaki Falasdinawa, wajen sake gina manyan kayayyakin more rayuwa na likitanci, ta yadda za a inganta ci gaban fannin kiwon lafiyar Falasdinu.
Na uku, a yi kokarin “Kafa kasashe biyu”. Wato ya kamata a gaggauta sake fara tattaunawa kan batun shimfida zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila, da sa kaimi wajen hanzarta aiwatar da manufar “Kafa kasashe biyu” kamar yadda ya kamata, da tabbatar da ‘yancin al’ummar Falasdinu na kafa wata kasarsu, da kasancewarsu, da kuma na komarwasu a yankin. (Safiyah Ma)