Jakadu da wakilai na dindindin a MDD da sauran hukumomin kasa da kasa dake Vienna na kasashe 8, sun bayyana muhimmancin hadin gwiwa wajen amfani da fasahohin nukiliya ta hanyar lumana.
Wakilan daga kasashen Ghana da Brazil da Namibia da Bangaladesh da Nijeriya da Pakistan da Venezuela da kuma Indonesia, sun bayyana haka ne yayin rangadin da suka yi a kasar Sin, inda suka ziyarci wuraren kirkire-kirkire da nune-nunen fasahohin nukiliya na Sin dake lardin Shandong na gabashin kasar da kuma birnin Beijing.
Wakilan sun kuma yi musayar ra’ayi da jami’ai Sinawa da masana wadanda suka halarci taron karawa juna sani kan amfani da fasahohin nukiliya ta hanyar lumana da ya gudana a birnin Beijing.
Taron wanda hukumar kula da makamashin nukiliya ta Sin CAEA da ofishin tawagar Sin a MDD da sauran hukumomi dake Vienna suka shirya, ya gudana ne daga ranar 22 zuwa 27 ga watan nan na Yuni.
Wakilan na kasashen waje sun ce ci gaban Sin a fannin makamashin nukiliya da fasahohinsa sun ja hankalin kasa da kasa, suna cewa Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana a tsakanin kasashe masu tasowa.
A nata bangare hukumar CAEA ta ce za ta hada hannu da hukumar kula da makamashin nukuliya ta duniya IAEA da sauran abokan hulda daga kasashe masu tasowa, wajen inganta kirkire-kirkire da raya makamashin nukiliya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp