Kasar Jamaica na fatan ganin tsohon dan kwallon Manchester United wanda yanzu haka ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Getafe, Mason Greenwood ya koma wakiltarta a wasannin kasashe.
Greenwood wanda ya shafe shekara daya ba tare da ya buga kwallo ba sakamakon wata shari’a da aka yi da shi yanzu haka yana buga kwallo a Getafe.
- Zulum Ya Daukaka Darajar Kwalejin Larabci Zuwa Babbar Cibiyar Yaki Da Akidun Boko Haram
- Kisan Dan Jarida: ‘Yansandan Sun Kama Wadanda ake Zargi Da Hannu A Zamfara
Wasa daya Greenwood ya wakilci kasar Ingila, kenan idan Jamaica ta yi kamun kafa a wajen hukumar kwallon kafa ta FIFA zai iya wakiltarta.