Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta bankaɗo dalibai 3000 da suka kammala karatun bogi, wadanda ba su taba taka kafa a aji don ɗaukan karatu ba.
Hukumar ta kuma yi Allah wadai da yadda wasu makarantu ke bayar da gurbin karatu ba bisa ka’iɗa ba, wanda a cewarta, hakan na ci gaba da zama abin kunya ga kasar nan.
- Tinubu Zai Halarci Zikirin Juma’a A Fadar Aminu Ado Ta Nassarawa
- Minista Ya Kaddamar Aikin Titi Mai Tsawon Kilomita 1000 Daga Sakkwato, Kebbi Zuwa Legas
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne, ya sanar da hakan ga shugabannin kwamitin kula da jami’o’in kamar rahoton da hukumar ya tabbatar.
A watan Disambar 2023, Kwamitin majalisar wakilai mai kula da ilimin bai daya ya umarci hukumar JAMB da ta gabatar da jerin sunayen manyan makarantun da suka gudanar da jarabawar shiga jami’a ba bisa ka’ida ba.
A baya dai hukumar jarabawar ta gargadi ɗalibai da su guji karbar gurbin karatu ko shaidar kammala karatu daga irin waɗannan jami’o’in da ke bayar da shaida ba tare da cikakken halartar karatu ba.