Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta gano akalla 585 jabun takardun shaidar kammala sakandire a shekarar 2025 kaɗai.
Shugaban hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede ne ya bayyana hakan a yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan Hukumar a shirye-shiryen zana jarabawar 2025 (Mock UTME da UTME).
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Karkashin Jagorancin Sowore A Abuja
- Ƴansanda Sun Janye Gayyatar Sarki Sunusi, Zasu Zo Kano Da Kansu
Oloyede ya bayyana cewa, an samar da tsarin tantance bayanan ilimin gaba da sakandare na Nijeriya ne (NIPED) don bankaɗo irin wannan kalubalen.
Ya kuma kara da cewa, binciken farko ya nuna cewa, da sa hannun ma’aikatan hukumar ake tafka wannan aika-aika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp